Buratai fa so yayi a mika masa Igboho, amma gwamnatin kasar Benin taki: Femi Falana
1 - tsawon mintuna
Shahrarren Lauya, Femi Falana, ya bayyana yadda gwamnatin jamhuriyyar Benin ta watsawa Ambasadan Najeriya dake kasar, Tukur Buratai, kasa a ido.
Falana yace hakan ya faru ne lokacin da hukumomin kasar suka bayyanawa Buratai cewa zasu bi doka ne wajen mayar da Sunday Igboho Najeriya.
Igboho wanda ke daure a kurkukun jamhurriyar Benin yanzu ya shiga hannun hukumar Kotono ne ranar 19 ga Yuli yayinda yake kokarin guduwa kasar Jamus.
Me ya faru tsakanin Buratai da gwamnatin kasar Benin?
Femi Falana, yayinda hira a shirin Politics na tashar ChannelsTV ranar Alhamis, ya bayyana cewa Tukur Burati ya bukaci a mika masa Igboho.
Yace: "Abinda ya kamata shine gwamnatin Najeriya ta aike wasikar bukata ga gwamnatin jamhurriyar Benin amma Jakadan Najeriya, Janar Yusuf Buratai (mai murabus), wanda ko a lokacin bai aike wasikar sanar da Benin yana kasar ba ya bukaci a mika masa Igboho."
"Sai suka ce masa, 'kayi hakuri, muna bin doka anan'. Wannan shine dalilin da yasa lamarin ke kotu har yanzu."
Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari
Asali: Legit.ng