Ba mu da labarin cinikin sayan makaman $875m hannun Amurka: Lai Mohammed

Ba mu da labarin cinikin sayan makaman $875m hannun Amurka: Lai Mohammed

  • Tsakanin gwamnatin Najeriya da Amurka, wa ke fadin gaskiya?
  • Amurka tace fasa sayarwa Najeriya makaman biliyoyin Naira amma Najeriya tace ai ita bata nemi wasu makamai daga wajenta ba
  • Ministan Labaran Najeriya yace labarin bogi ne

Gwamnatin tarayya ta yi martani kan jawabin yan majalisar dokokin Amurka na hana sayarwa Najeriya wasu jirage da makamai saboda zaluncin mulkin Buhari.

Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed yace a iyakan saninsa babu wata maganar cinikayyar sayar makaman $875m tsakanin Najeriya da Amurka kamar yadda ake yadawa.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da kamfanin dillanci labaran Najeriya NAN ranar Juma'a a Abuja.

Lai Mohammed ya jaddada cewa babu watan kwantiragin makamai tsakanin Najeriya da Amurka.

A cewarsa:

"Babu wani kwantiragin sayan makamai tsakanin Najeriya da Amurka a yau sabanin jiragen Super Tucano 12, wanda shida sun iso."
"Bamu da masaniya kan wani cinikin $875m ko wasu jirage masu saukar angulu da aka ce wasu yan majalisan Amurka na kokarin hana shugaban kasan hana sayarwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Mu San Da Wani Kwangilar Siyan Makamai Na $875m Daga Amurka Ba, FG

"Alakar da ke tsakanin Najeriya da Amurka na kara karfi kuma babu wata matsala."

Ba mu da labarin cinikin sayan makaman $875m hannun Amurka: Ministan Labarai
Ba mu da labarin cinikin sayan makaman $875m hannun Amurka: Lai Mohammed Hoto: Ministry of Information and Culture
Asali: Facebook

Ba zamu sayarwa Najeriya makamai ba saboda zaluncin da jami'anta keyi: Yan Majalisar Amurka

Yan majalisar dokokin Amurka sun hana sayarwa Najeriya jiragen yaki masu saukar angulu bisa zalunci da take hakkin bil-adama da gwamnatin Buhari tayi.

Cinikayyar da aka yi na kudi $875million don sayan jiragen Cobra attack helicopter guda 12 ya fuskanci kalubale ne yayinda zaman kwamitin majalisar dattawa na harkokin wajen Amurka.

Jawabin da aka saki a shafin kwamitin na yanar gizo ya nuna cewa ma'aikatar wajen Amurka ce ta fara aikewa majalisa rahoton cinikin a Junairu kafin nada Joe Biden matsayin shugaban kasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel