Kwatanta Annabi Musa da Annabi Muhammadu da Igboho: MURIC ta caccaki kungiyar Afenifere

Kwatanta Annabi Musa da Annabi Muhammadu da Igboho: MURIC ta caccaki kungiyar Afenifere

  • An bukaci kungiyar Afenifere ta nemi gafara kan kwatanta Sunday Igboho da Annabi Musa da Annabi Muhammad (SAW)
  • Kungiyar MURIC ta ce ba za'a taba amincewa da wannan abu da Afenifere tayi ba
  • MURIC tayi kira ga dukkan Musulmi Bayarabe da ya nisanta kansa daga rajin neman kafa kasar Oduduwa

Lagos - Kungiyar kare hakkin Musulmai MURIC ta caccaki kungiyar Yarabawa, Afenifere, kan kwatanta Hijrar fiyayyen hallita da na mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho.

A ranar Litinin, Afenifere yace babu laifi kan guduwar da dan gargajiya Sunday Igboho yayi saboda wasu manzanni sun gudu daga garuruwansu lokacin da suka fuskanci matsin lamba.

A jawabin da Diraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya saki ranar Talata, ya ce abinda ya haifar da Hijrar manzannin Allah ya sha banban da na Igboho.

Akintola yace:

"Wannan rainin hankali ne. Wannan wuce gona da iri ne. Afenifere ta nunawa duniya cewa ita yar gargajiya ce kuma wannan yunkurin tayar da tarzoma ne."

Kara karanta wannan

Lauya ya bayyana laifuka 3 da gwamnatin Buhari ke tuhumar Sunday Igboho akai

"Abinda ya sa Manzon Allah (SAW) yayi Hijra zuwa Madina ya banbanta sosai da abinda ya kori Igboho zuwa jamhurriyar Benin a Yulin 2021."

Kwatanta Annabi Musa da Annabi Muhammadu da Igboho: MURIC ta caccaki Afenifere
Kwatanta Annabi Musa da Annabi Muhammadu da Igboho: MURIC ta caccaki kungiyar Afenifere Hoto: Professor Ishaq Akintola
Asali: Facebook

Duk Musulmin dake goyon bayan Igboho ya janye

Diraktan MURIC ya kara da cewa dukkan Musulmai masu goyon bayan kafa kasar Yoruba su janye daga hakan. Ya ce wajibi ne hakan.

Yace:

"MURIC na kira ga Yarbawa Musulmai masu goyon bayan kafa kasar Oduduwa su janye da wuri idan sun yi Imani da Allah da Annabi Muhammadu. Ba zamu bi wadanda ke cin mutuncin annabinmu ba."
"Babu Musulmin gaskiya da zai yi hakan. Sun san illan haka a addini. Duk Musulmin da ya ki janyewa yakin kafa kasar Oduduwa bayan Afenifere ta zagi Manzon Allah to ya shirya hisabi gaban Allah ranar Al-Qiyamah."
"Wannan ba fatawa bane. Wannan koyarwan addinin Musulunci ne cewa kowani Musulmi ya janye daga masu tsangwamar addininsa."

Kara karanta wannan

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

Sunday Igboho ya ji mummunan rauni

Mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho, ya samu munanan raunuka lokacin da jami'an hukumar DSS suka kai masa hari gidansa dake Soka, Ibadan, jihar Oyo.

A ranar Alhamis, 1 ga Yuli, 2021, hukumar DSS ta kai samame gidan Igboho.

Lauyansa na kasar Benin, Ibrahim Salami, ya bayyana hakan a hirar da yayi ranar Talata, rahoton ThePunch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel