Ramuwar gayya: ‘Yan bindiga sun auka wa wani kauye a Zamfara, sun hallaka dinbin mutane

Ramuwar gayya: ‘Yan bindiga sun auka wa wani kauye a Zamfara, sun hallaka dinbin mutane

  • ‘Yan bindiga sun shiga karamar hukumar Zurmi, sun hallaka mutane da yawa
  • Kwanakin baya aka kashe ‘Yan bindigan, don haka suka zo daukar fansa jiya
  • Wadannan miyagun mutane sun tsere da shanu da dabbobin mutane daga Jaya

A ranar Litinin dinnan, 27 ga watan Yuli, 2021, wasu ‘yan bindiga su ka dura kauyen Jaya a yankin Boko, karamar hukumar Zurmi, da ke jihar Zamfara.

Jaridar Daily Trust ta ce wadannan ‘yan bindiga sun kashe da-dama daga cikin mazauna Jaya.

Wasu wadanda abin ya wakana a kan idanunsu, sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun shigo garin Jaya ne a saman babura da 100 a jiya.

“Sun kuma dauke shanu da wasu dabbobi. Na ga mutane uku da aka yi wa rauni za a kai su asibiti a garin Boko. An harbe su a hannu, kafafu, da cinyoyi.”

Majiyar ta shaida cewa ba a iya duba wadannan mutane da aka harba a Boko ba. Asibitin sun tura zuwa wani babban asibiti a birni da su ke da kayan aiki.

Kara karanta wannan

Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna

“Kwanakin baya, ‘yan bindigan sun yi yunkurin kai hari a wani gari, sai ‘yan banga suka kai sameme, ‘yan bindigan suka tsere da aka kashe wasu.”
‘Yan bindiga
Gungun 'Yan bindiga Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Bisa dukkan alamu, abin da ya faru ya bata wa ‘yan bindigan rai, don haka suka kara yin shiri, su ka duro wa kauyuka. Sun zo a kan babura sama da 100.”
“Lokacin da suka auka wa jama’a, sai kowa ya yi ta kokarin ya boye kansa a cikin gidansa.”

Kamar yadda rahoton ya bayyana mana, wannan gari na Jaya ya tara kauyuka da ke gabas da Boko.

Wani mazaunin yankin ya ce yara da mata rututu sun tsere daga kauyukan, wasunsu sun iso garin Boko da yammacin jiya, duk da ruwan da ake ta tsula wa.

A dalilin matsalar rashin tsaro ne aka ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da duk makarantu daga koma wa daga hutun sallah har sai sun ji sanarwa.

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Da yake jawabi, Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i yace gwamnatinsa ta ɗauki wannan matakin ne domin a ba dakarun sojoji damar yin aikin da su ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel