Ina Rayuwa a Karamin Gida Cikin Talakawa, Gwamna Ya Fadi Inda Yake Rayuwa Duk da Matsayinsa

Ina Rayuwa a Karamin Gida Cikin Talakawa, Gwamna Ya Fadi Inda Yake Rayuwa Duk da Matsayinsa

  • Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, yace yana rayuwa ne a cikin gida mai dakin kwana uku kacal
  • Gwamnan yace dole akwai wata rana da zai bar mulki, shiyasa yake rayuwa cikin talakawansa
  • A cewarsa babu wanda yasan wazai lashe zaɓen gwamna dake tafe a shekarar 2023 sai Allah

Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia, yace yana rayuwa ne a gida mai ɗakin kwana uku a Aba, babbar cibiyar kasuwancin jihar, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamna ya faɗi haka ne yayin wata fira da yayi da manema labarai ranar Litinin.

Ya ƙara da cewa ya zaɓi rayuwa a cikin mutanen da yake mulka ne domin yasan akwai wata rayuwar bayan ya kammala mulki.

Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu
Ina Rayuwa a Karamin Gida Cikin Talakawa, Gwamna Ya Fadi Inda Yake Rayuwa Duk da Matsayinsa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace: "Bana son in mance da asalin yadda nake rayuwa a baya. Zan yi aiki tukuru ta yadda wanda zai gaje ni zai sha walaha idan ba hanyar dana bi zai amfani da ita ba."

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: El-Rufa'i Ya Dakatad da Komawa Makaranta a Jihar Kaduna Sai Baba Ta Gani

Okezie Ikpeazu yace mulki babban abu ne mai muhimmanci, wanda ubangiji ba zai iya sakarwa mutane shi baki ɗaya ba.

Wa zai gaji gwamnan Abia a 2023

Gwamna Ikpeazu yace tambayar da ake masa cewa waye zai gaje shi a 2023 babu mai iya amsa ta sai ubangiji.

Amma gwamnan ya bayyana fatan shi cewa duk wanda zai gaje shi ya ɗora daga inda ya tsaya, kuma yayi abinda yafi na shi.

Yace: "Duk wanda yake a matsayin da nike a yanzun zai so ace wanda zai gaje shi ya ɗora daga inda ya tsaya kuma ya nufi al'ummar jihar mu da alheri sannan kuma yayi abinda ni da ya gada ban yi ba."

"A kowane irin lokaci a matsayina na gwamna, ina kara jaddada cewa akwai wasu abubuwa masu muhimmanci da ya kamata mu aiwatar matukar muna son ci gaba."

A wani labarin kuma Ku Tona Min Asiri Idan Har Na Saci Kuɗin Talakawa, Gwamnan Nigeria Ya Faɗa Wa Masu Zarginsa

Kara karanta wannan

Bana Bukatar Ko Sisin Kobo Daga Hannunku, Shugaba Buhari Ga Yan Kwangila

Owerri, Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce bai taba satar kudin al'umma ba tun lokacin da ya kama aiki a matsayin gwamna a jiharsa.

The Nation ta ruwaito cewa a ranar Asabar 24 ga watan Yuli, gwamnan ya kallubalanci mutanen jihar su fallasa shi idan ya taba karkatar da kudaden al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262