Shari'ar Kanu: An saki Sowore da magoya bayan Nnamdi Kanu bayan sun ci duka
- Rahoto ya bayyana cewa, an saki mawallafin jaridar SaharaReporters da wasu mutane da aka kame
- A yau ne aka kame Sowore tare da wasu mutane da suka hallara a bakin babbar kotun tarayya dake Abuja
- Sun bayyana abubuwan da suka fuskanta a hannun 'yan sanda na cin zarafi da mummunan hali
Rahoto ya bayyana cewa, an saki mawallafin jaridar SaharaReporters Omoyele Sowore da wasu da aka kama yayin wata zanga-zanga a Babbar Kotun Tarayya, jaridar Punch ta ruwaito.
Masu fafutukar sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar shari'a a kotu.
‘Yan sa’o’i kadan bayan kamasu, dan fafutukar 'Buhari-Must-Go' ya sanar da cewa an sake shi tare da wasu.
Ya ce:
“Yanzu haka sun sake mu. Sun ja mu, sun wulakanta mu kuma sun doke mu.
“Sun kai mu ofishin 'yan sanda na sakatariyar tarayya. Na gaya musu cewa ba su da ikon kama ni.
“Ina da 'yancin kallon shari’ar Nnamdi Kanu. Sun karbe katunanmu sun goge dukkan bayanan da muka dauka.”
Gamayyar kungiyoyin farar hula sun yi Allah wadai da kame Sowore
Jaridar The Nation ta tattaro cewa, gamayyar kungiyoyin farar hula sun yi martani tare da yin Allah wadai da kamun Sowore da wasu magoya bayan shugaban IPOB da aka tsare, Nnamdi Kanu.
Gamayyar ta ce:
“Mun yi Allah wadai da wannan kamen a zaman wani bangare na ci gaba da maida kasar cikin wani mummunan hali na danniyar sojoji.
"Ba abu ne mai karbuwa ba kwata-kwata kuma muna yin kira ga dukkan 'yan Najeriya masu sha'awar kiyaye dimokiradiyyar kasar nan da su yi Allah wadai da wannan kamen kan 'yan jarida, kan masu fafutuka da lauyoyi a yau a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
'Yan Sanda Sun Cafke 'Yan IPOB a Wurin Shari'ar Nnamdi Kanu
A wani labarin, ‘yan sanda a ranar Litinin sun fatattaki wasu mambobin kungiyar IPOB wadanda suka mamaye Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja don jin yadda za ta kaya a shari’ar Nnamdi Kanu, shugabansu.
Mambobin kungiyar da suka fusata sun mamaye kotun gabanin shari’ar tasa, inda wani rahoton The Cable ya ce tuni an kame wasu daga cikin mambobin na IPOB.
‘Yan kungiyar IPOB din suna ta rera taken nuna goyon baya ga Kanu tare da neman a sake shi.
Asali: Legit.ng