Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Cafke Wani Jami'in Dan Sanda da Tarin Alburusai da Gurneti a Borno

Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Cafke Wani Jami'in Dan Sanda da Tarin Alburusai da Gurneti a Borno

  • Sojojin Operation Hadin kai sun damke wani mutum, Ebenezer Ojeh, ɗauke da alburusai da gurneti a jihar Borno
  • Yayin tuhumar wanda sojojin suka kama, ya bayyana cewa jami'in ɗan sanda ne reshen jihar Rivers
  • A halin yanzun sojojin sun tafi da shi hedkwatarsu domin gudanar da bincike

Dakarun sojin Operation haɗin kai na rundunar sojojin ƙasa ta cafke wani da ake zargin ɗan sanda ne, Ebenezer Ojeh, ɗauke da tarin alburusai a jihar Borno, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Sojojin bataliyar Ngamdu, sun damke sajan ɗin yan sandan ne a wurin binciken abun hawa dake kan hanyar Maiduguri-Damaturu, bisa jagorancin Manjo D.Y Chiwar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Wani jami'in soja ya bayyana wanda ake zargin mai lambar yan sanda No: 456647 yana cikin wata motar Bus ta Borno dake kan hanyar zuwa Abuja yayin da suka iso wajen binciken.

Sojoji sun kama.dan sanda da alburusai a Borno
Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Cafke Wani Jami'in Dan Sanda da Tarin Alburusai da Gurneti a Borno Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Jami'in sojin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace lokacin da motar ke jiran sojoji su gama binciken ta, sai wanda ake zargin ya fito daga motar da nufin yaje biyan buƙata.

Kara karanta wannan

Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno

Yace: "Wannan dalilin ne yasa kwamandan dake wajen ya umarci sojoji su binciki jakarsa domin bai yarɗa da shi ba."

"Yayin duba jakar ne sojojin suka ga alburusai akalla 220 da kuma gurneti ɗaya, da kuma wasu makamai."

Shin dagaske dan sanda ne?

Yayin da sojojin suka fara tuhumarsa, Mr. Ojeh, yayi ikirarin cewa jami'in ɗan sanda ne a runduna ta musamman da aka fi sani da SWAT reshen jihar Rivers.

A halin yanzun sojojin sun tasa ƙeyar wanda ake zargin zuwa hedkwatar operation haɗin kai sashi na biyu domin cigaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel