Hukunci yin Sallolin Farilla 5 akan Lokaci, Tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hukunci yin Sallolin Farilla 5 akan Lokaci, Tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malam ya yi bayani kan muhimmancin Sallah a kan lokaci.

Wajibi ne yin salloli biyar a kan dukkan baligi, mai hankali a halin zaman gida, halin tafiya da yaƙi a kan namiji da mace, sai mace mai yin jinin haila, da mai jinin biƙi har sai ya ɗauke.

Ana umartar yaro da yin sallah tun yana ɗan shekara bakwai domin ya saba, saboda faɗin Allah ﷻ a cikin Suratul Nisa`i:

﴿ إِنَّ الصَّلَوةَ كَانَتْ عَلَى المُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَوْقُوتًا ﴾ ()

Ma’ana: “Haƙiƙa sallah ta kasance wajibi ce a kan muminai kuma an saka mata lokaci.” Da kuma faɗinSa a cikin Suratul Baqarah:

﴿ حَافِظُواْ عَلَى الصَّلَوَتِ وَالصَّلَوةِ الْوُسْطَى ﴾ ()

Ma’ana: “Ku kiyaye salloli da kuma sallar tsakiya.” ()

Hukunci yin Sallolin Farilla 5 akan Lokaci, Tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Hukunci yin Sallolin Farilla 5 akan Lokaci, Tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Mal.Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Abdullahi Ɗan Umar (رضي الله عنه) cewa Manzon Allah ﷺ ya ce,

“An gina Musulunci a kan ginshaƙai guda biyar: Shaidawa babu abin bauta bisa cancanta da gaskiya sai Allah ﷻ, kuma Annabi Muhammad ﷺ ManzonSa ne, da tsayar da sallah da bayar da zakka da hajji da azumin watan Ramadan.”

Da hadisin Abdullahi ɗan Abbas (رضي الله عنه) ya ce,

“Lokacin da Annabi ﷺ ya tura Mu'azu zuwa Qasar Yamen ya ce masa, “Ka kirawo su zuwa ga shaidawa babu Abin bauta bisa cancanta da gaskiya sai Allah ﷻ kuma su shaida ni ManzonSa ne. Idan sun yi biyayya ga haka, ka ce musu: Haqiqa Allah ﷻ Ya wajabta musu yin salloli biyar dare da rana.”

Haka kuma hadisin Amri Bn Shu’aib wanda Al'Imam Ahmad da Abu Dawud suka ruwaito, Manzon Allah ﷺ ya ce,

“Ku umarci ‘ya’yanku da yin sallah, tun suna ‘yan shekara bakwai, ku yi musu ladabi a kan sallah idan suka kai shekara goma, kuma ku raba musu shimfiɗa a wajan bacci.” () (Wato ya zama kowa wajen kwanansa daban).

Alamomin da za a gane yaro ko yarinya sun balaga na farko idan suka cika shekara goma sha biyar, na biyu idan gashin hammata ko gashin gaba ya tsiro musu, ko kuma suka kwanta bacci suka yi mafarki maniyyi ya fito.

Idan kuma namiji aka ga ya fara gemu da gashin baki, ko kuma mace aka ga ta fara yin jinin haila, ko ta ɗauki ciki, duk waɗannan su ne alamomin balaga. Idan suka bayyana alqalamin Shari'a ya hau kan mutum, mace ko namiji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel