Jerin jamio'i 3 mafi inganci a fagen masana ilimin kimiyya a Najeriya
- Alkaluman cibiyar AD sun nunar da jami’o’in Najeriya uku ne suka yi zarra a Afirka da kuma duniya
- Cibiyar ta ce ta yi la’akari da kwarewar jami’o’in wajen janyo masana kimiyyar
- Jami’ar Cape Town da ke Afirka ta Kudu ce ta yi zarra a Afirka
Jami'ar Ibadan (UI), da Jami'ar Najeriya, Nsukka (UNN), da Jami'ar Ilorin (UNILORIN) sun zama kan gaba dangane da masana kimiyya mafi inganci a Najeriya.
Cibiyar AD Scientific Index, wacce take kan gaba ta fuskar fitar da alkaluman kwazon jami’o’i a duniya wanda ke da mazauni a Turkiyya, a kwanakin baya ne ya fitar da jerin sunayen kwararrun masana kimiya da jami’o’i na duniya da suka yi zarra na shekarar 2021.
Kamar yadda jerin ya nunar Jami’ar UI ta kasance ta 19 a nahiyar Afirka kuma ta 1,350 a duniya yayin da Jami’ar UNN ta kasance ta 25 a cikin nahiyar kuma ta 1,522 a duniya.
Jami’ar UNILORIN kuma ta kasance ta 41 a Afirka sannan ta 1,941 a duniya. Jami'ar Fasaha ta Tarayya, da ke Akure (FUTA) ita ce ta zo ta hudu yayin da Jami'ar Calabar (UNICAL) ta zama ta biyar mafi inganci a Najeriya a kan matsayin.
Cibiyar AD Scientific Index ta ce matsayin "ya nuna kwarewar jami’o’in wajen jawo hankalin masana kimiyyar da kuma karfin cibiyoyi ta fuskar karfafa ci gaba da rike masana kimiyyar."
Jami'ar Harvard ita ce kan gaba a duniya kamar yadda jerin ya nunar yayin da Jami'ar Cape Town da ke kasar Afirka ta Kudu ta kasance jagaba a Afirka.
A nan kasa, jerin jami’o’in Najeriya ne bisa ingancin ilimin kimiyyar a kamar yadda alkaluman shekarar 2021.
Ga Jerin Jami'o'in
1. Jami'ar Ibadan (UI)
2. Jamiar Nigeria, Nsukka (UNN)
3. Jami'ar Ilorin (UNILORIN)
4. Jami'ar Fasaha, Akure (FUTA)
5. Jami'ar Calabar (UNICAL)
6. Jami'ar Ahmadu Bello Zaria
7. Jami'ar Benin (UNIBEN)
8. Jami'ar Port Harcourt (UNIPORT)
9. Jami'ar Lagos (UNILAG)
10. Jami'ar Obafemi Awolowo
11. Jami'ar Ladoke Akintola LAUTECH
12. Jami'ar Fasaha, Owerri
13. Jami'ar Jihar Legas
14. Jami'ar Usman Danfodiyo
15. Jami'ar ilmin Likitanci na Legas
16. Jami'ar Redeemer’s
17. Jami'ar Kimiya da Fasaha ta Africa Abuja
18. Jami'ar Skyline
19. Jami'ar Covenant
20. Jami'arNnamdi Azikiwe
21. Jami'ar Fasaha ta Minna FUT
22. Jami'ar Uyo
23. Jami'ar jihar Delta
24. Jami'ar Bayero Kano
25. Jami'ar jihar Ekiti
26. Jami'ar Landmark
27. Jami'ar Maidugri
28. Jami'ar Abuja
29. Jami'ar Jos
30. Jami'ar Oye Ekiti
31. Jami'ar Ndufu Alike Ikwo (FUNAI)
32. Jami'ar Olabisi Onabanjo
33. Olabisi Onabanjo jihar Osun
34. Olabisi Onabanjo Abubakar Tafawa Balewa
35. Jami'ar jihar Akwa Ibom
36. Jami'ar jihar Kwara
37. Jami'ar fasahar Modibbo Adama Yola
38. Jami'ar tarayya Dutsin Ma
39. Jami'ar Adekunle Ajasin
40 Jami'ar jihar Edo Iyamho
41. Jami'ar Amurka a Najeriya
42. Jami'ar Neja Delta
43. Jami'ar tarayya dake Wukari, Taraba
44. Jami'ar jihar Ebonyi
45. Jami'ar jihar Nasarawa
46. Jami'ar Elizade Ilara Mokin
47. Jami'ar Bowen
48.Jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu
49. Jami'ar tarayya dake Dutse Jigawa
Asali: Legit.ng