Masanin Tattalin arziki a Amurka ya kwatanta Shugaban Najeriya a zaman mai kasala

Masanin Tattalin arziki a Amurka ya kwatanta Shugaban Najeriya a zaman mai kasala

  • Masanin tattalin arzikin Ba’amurke ya soki lamirin gwamnatin Buhari da gaza magance matsalolin Najeriya
  • Ya yi kaurin suna a sukar gwamnatin Buhari
  • Ya kwatanta Buhari a zaman mai kasala kuma gajiyayye

Wani Ba’amurke masanin tattalin arziki a Jami’ar John Hopkins da ke Baltimore a Amurka, Steve Hanke, ya caccaki gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta kan kasala da rashin iya aiki wajen magance matsalolin tsaro na Najeriya.

Hanke, wanda ya yi kaurin suna a caccakar gwamnatin Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake martani kan harin da aka kai wa jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya na kwanan nan wanda ‘yan bindiga suka yi yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Hanke ya yi martani ne kan baro jirgin yakin Sojoji da yan bindigan Zamfara suka yi makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

Masanin Tattalin arziki ya caccaki Shugaban Najeriya a zaman mai kasala
Masanin Tattalin arziki a Amurka ya kwatanta Shugaban Najeriya a zaman mai kasala Hoto: DailyPost
Asali: Facebook

A jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis, Hanke, ya caccaki Buhari kan yadda ya bari yan bindiga suka cigaba da addabar mutanen Najeriya.

Yace:

"Najeriya ce ta 161 cikin kasashe 162 a jerin masu fuskantar matsalar tsaro, bisa rahoton da Caton Institue ta saki kwanan nan."
"A iyakar jihar Kaduna, yan bindiga sun baro jirgin yakin Sojin sama."
"Kuma duk karkashin mulkin gajiyayye Buhari, yan bindiga na cin karnukansu ba babbaka."

Tsohon abokin Buhari ya caccakesa

Tunde Bakare, shugaban cocin Citadel Global Community, ya ce Ubangiji ya juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

A yayin jawabi a cocinsa wacce a da aka sani da Latter Rain Assembly, Bakare yace zai yi fito-na-fito da shugaban kasa kuma ya ga wanda zai bibiyesa kamar yadda aka saba yi wa duk wanda yayi magana a kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel