Daga Karshe, Gwamnan Cross River ya bayyana dalilin da yasa ya koma jam'iyyar APC

Daga Karshe, Gwamnan Cross River ya bayyana dalilin da yasa ya koma jam'iyyar APC

  • Gwamna Ben Ayade ranar Alhamis, 22 ga Yuli, ya bayyana cewa halayen Buhari suka ja hankalinsa zuwa APC
  • Gwamnan na Cross Ribas ya bayyana cewa gaskiyar Buhari da saukin kansa ababe biyu ne masu tsada
  • Ayade yace har yanzu babu wanda ya taba tuhumar shugaban kasan da sata da almundahana

Makonni bayan sauya shekarsa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Gwamna Ben Ayade na Cross River ya fara bayyana dalilan da suka sa ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Ayade a ranar Alhamis, 22 ga Yuli, ya bayyana cewa halayyan shugaba Buhari irinsu gaskiya da saukin kai suka sa shi fara sha'awar shiga jam'iyyar APC, rahoton TheNation.

Gwamna Ayade ya kara da cewa gabanin zama shugaban kasa, Buhari ya zauna a gidansa guda daya na tsawon shekaru 30, hakan na nuna cewa mutum ne mai tarbiyya.

Yace:

"Buhari ya janyo ni APC ta saukin kansa da gaskiyarsa, da kyar da samu irin wadannan dabi'u cikin mutane."

Kara karanta wannan

Adalcin Shugaba Buhari da Saukin Kansa Yasa Na Sauya Sheka Zuwa APC, Gwamna

"Misalin, shugaban kasa ya zauna a gida daya na tsawon shekaru 30, duk da ya zama shugaban kasa sau biyu, har yanzu yana zaune a gidan kuma babu almundahana da sata."

Ayade ya kara da cewa shugaba Buhari yayi alkawarin daukar nauyi da cigaba da wasu ayyukan da gwamnatinsa ta fara.

Daga Karshe, Gwamnan Cross River ya bayyana dalilin da yasa ya koma jam'iyyar APC
Daga Karshe, Gwamnan Cross River ya bayyana dalilin da yasa ya koma jam'iyyar APC Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

Gwamnonin Jam’iyyar PDP a Arewa suka yi zargin cewa Gwamnatin Muhammadu tana razanar da su da sauran mambobin jam’iyyar adawa domin su shiga Jam’iyyar APC.

Sun yi ikirarin cewa wadansu takwarorin nasu, ciki har da Ben Ayade Gwamnan Jihar Kuros Riba da Bello Matawalle Gwamnan Jihar Zamfara, wasan a kwanan baya suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki sun yi hakan ba da son ransu ba.

Gwamnonin PDPn sun kuma zargi Gwamnatin Buhari da yi wa Arewa kwange duk kuwa da cewa ita ce iko a siyasance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel