Ko gobe a shirye na ke in sake tsayawa Nnmadi Kanu a kotu inji Sanatan Abia, Abaribe

Ko gobe a shirye na ke in sake tsayawa Nnmadi Kanu a kotu inji Sanatan Abia, Abaribe

Sanata Enyinaya Abaribe ya ce har gobe zai iya tsaya wa Nnamdi Kanu a kotu

Enyinaya Abaribe ya yi bayanin abin da ya sa Kanu ya tsere bayan ya samu beli

Sanatan ya ce bai yi nadamar kare mutumin jiharsa a kotun duk da ya tsere ba

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan Najeriya, Enyinaya Abaribe, ya ce zai tsaya wa Nnamdi Kanu a kotu idan har akwai bukatar ayi hakan.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Enyinaya Abaribe bai dandara a kan abin da ya yi a baya ba.

Sanata Enyinaya Abaribe ya tsaya wa Mazi Nnamdi Kanu a kotu, har aka samu aka ba shi beli. Amma a 2017, shugaban na IPOB, ya sulale, ya bar kasar.

Da aka yi hira da shi a wani shiri a gidan talabijin na TVC, ‘dan majalisar ya bayyana abin da ya sa ya tsaya wa Kanu a lokacin da ake shari’a da shi a kotu.

Kara karanta wannan

Babu wani riba da Buhari ke samu, ba zai yarda da zango na uku ba - Yerima Abdullahi

Kotu ta shardanta ni zan karbi belin Nnamdi Kanu - Abaribe

Sanatan yake cewa kotu ce ta ce dole wanda zai tsaya wajen karbar belin wannan mutumi ya zama Sanata, kuma shugaban Sanatocin kudu maso gabas.

Enyinaya Abaribe ya ce wannan ya sa ya gabatar da kansa, domin ceto shugaban kungiyar IPOB.

Muddin akwai bukata, zan sake tsaya masa

Da aka tambaye shi ko zai iya sake tsaya wa Kanu a kotu, ‘dan majalisar dattawan ya nuna cewa babu abin da zai hana, muddin irin damar ta sake samu wa.

Nnamdi Kanu
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
Asali: UGC

“Idan yanayi ya kama irin haka, me zai hana? ’Dan mu ne. Daga jiharmu (Abia) ya fito. Shi (Kanu) ya fada da bakinsa, cewa ya tsere ne domin ya ceci rayuwarsa.”
“Akwai bamabanci tsakanin tsere wa da kuma ceton rai.”

Na koma kotu na yi ikirari cewa a doka, wadanda suka ga Nnmadi Kanu a karshe, su ne sojojin Najeriya, su ne suka dura gidan mahaifinsa, su za su fito da shi.”

Kara karanta wannan

Duk da ba ayi wa Ibo adalci a Najeriya, ba za mu goyi bayan Biyafara ba – Dattijon Neja Delta

Kuma Alkali ta karbi maganar Abaribe, ta ce nauyin gabatar da Nnamdi Kanu ba ya kansa. Wannan ya sa ba a bukaci a kama Sanatan da laifin guduwar ba.

Mun kawo maku rahoto cewa wasu ‘Yan Sanda sun huce takaici kan Gwamnan jihar Zamfara, sun yi masa ruwan zagi saboda wasu abokan aikinsu da aka kashe.

Rahotanni sun ce Gwamna Bello Maawalle ya sha zagi a bainar jama’a daga wajen ‘yan sanda saboda matsalar tsaro, suka ce ba ayi masu abin da ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng