Sojojin Najeriya sun fara farautar makasan Janar din Sojan Kasa
- Sojojin Najeriya na jimamin kisan Janar Hassan Ahmed, wanda shi ne Provost Marshall na Sojojin Najeriya
- Wadanda suka kashe babban jami’in sojan har yanzu hukumomin tsaro ba su kamo su ba
- Yankin Koton Karfe na Jihar Kogi inda aka kashe Janar din ya yi kaurin suna da hare-haren 'yan bindiga
Hukumomin tsaro sun fara bincike kan kisan wani Janal din soja, Hassan Ahmed, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja.
Kafar labarai ta PR Nigeria ta ruwaito cewa sojojin na Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun kaddamar da wani mummunan farmaki na hadin gwiwa a yankin Koton Karfe na Jihar Kogi, inda aka kai wa jami'in sojin hari.
‘Yar uwansa wacce take cikin motar tare da shi, rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da ita yayin da direbansa ya tsere.
Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa
Kwanan nan, hanyar Koton Karfe ta kasance matattarar 'yan fashi da makami, wadanda yawanci sukan addabi masu ababen hawa.
Baya ga yawan sace-sacen mutane, 'yan fashin suna karbar kudin fansa ga mutanen da suka sace a garuruwansu.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa marigayin Janal din shi ne tsohon mai mukamin Provost Marshall na rundunar sojojin Najeriya.
An yi jana'izarsa a Abuja
An binne Janal Ahmed ne a ranar Juma’a, 16 ga Yuli, cikin yanayi na girmamawa irinta soja da yabo a makabartar Barikin Lungi da ke Abuja, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce rundunar ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin.
Asali: Legit.ng