Jerin Lokuta 5 da aka taba soke gudanar da aikin Hajji a tarihi

Jerin Lokuta 5 da aka taba soke gudanar da aikin Hajji a tarihi

  • Sau tarin lokuta ana soke gudanar da aikin Hajji
  • Wasu lokutan rikice-rikicen siyasa sun haddasa soke gudanar da aikin Hajjin
  • Akwai shekarun da aka shafe shekara 7 a jere ba tare da an gudanar da ibadar Hajjin ba

Annobar COVID-19 da ake fama da ita a halin yanzu a duniya ta janyo takaita adadin alhazan da za su gudanar da aikin Hajj a karo na biyu.

Takaitawar ta haifar da karuwar yada "labaran karya" da ma "kagaggun shaci-fadi" na rashin hankali, duk kuwa da cewa an dauki matakin ne bayan dogon nazari a tsawon watanni tare da la’akari da sababbin bayanan da aka tattara kan yaduwar cutar da zimmar kare lafiyar mahajjatan har ma da duniya baki daya.

A wannan mukalar, Haramain ta tattara adadin lokutan da aka kayyade aikin Hajji bisa dalilai da dama amma mafi yawansu sun kasance ne saboda barkewar wata cutar ko annoba.

Kodayake an soke aikin Hajji sau da yawa a cikin karnoni, tun lokacin da aka kafa Masarautar Saudiyya a 1932, an hana Hajji sau biyu ne kacal wato a 2020 da 2021.

1. 865: Kisan kiyashi a Dutsen Arafat

A lokacin rigimarsa da Khalifancin Abbasawa da ke Bagadaza, Ismail bin Yousef, wanda aka fi sani da Al-Safak, ya kai hari a kan dutsen Arafat mai tsarki da ke fuskantar birnin Makka a shekara ta 865, inda ya yi wa mahajjata kisan gilla a can. Rikicin ya tilasta dakatar da aikin Hajji.

2. 930: Harin mutanen Al-Qarmati

A shekarar 930, Abu Taher al-Janabi, jagoran darikar Qarmatian da ke da mazauni a Bahrain, ya kaddamar da hari a kan birnin Makka.

Tarihi ya nuna cewa 'yan Qarmatian sun kashe mahajjata 30,000 a cikin birnin Makka mai alfarma sannan suka jefar da gawawwakin a cikin rijiyar Zamzam mai alfarma. Sun kuma yi wasoso a Babban Masallacin Harami tare da satar Dutsen Hajarul Aswad daga cikin Kaaba, sannan suka kai shi tsibirin Bahrain.

Daga nan aka dakatar da aikin Hajji na tsawon shekara 10 har sai da aka dawo da Dutsen na Hajarul Aswad zuwa Makka.

'Yan Qarmatian din mabiya mazhabar Shi'a ne wadanda suka yi imani da tsarin al'umma ta daidaito kuma suka yi imanin cewa aikin hajji a matsayin al'adar arna.

DUBA NAN: Bayan kin amincewa da aurensa, matashi ya sayawa budurwa tsaleliyar mota

Jerin Lokuta 5 da aka taba soke gudanar da aikin Hajji a tarihi
Jerin Lokuta 5 da aka taba soke gudanar da aikin Hajji a tarihi Hoto: Haramain
Asali: Facebook

KU KARANTA: Abin mamaki yayin da wani mutum ya kara aure da kudin tallafin da kungiya ta ba shi domin kula da ’ya’yansa

3. 983: Lokacin Halifancin Abbasid da Fatimid

Ita ma siyasa, ta sha dagula aikin Hajji. A cikin rikice-rikicen siyasa na 983 tsakanin sarakunan halifofi biyu - Abbasiyawa na Iraki da Siriya da Fatimiyawa na Misira - sun haifar da cikas ga Musulmin da ke tafiya Makka domin aikin Hajji. Sai da aka shafe shekara takwas kafin a sake gudanar da aikin Hajji wato sai a cikin 991.

4. 1831: Annoba

Ba wai kawai rikice-rikice da kashe-kashe ne suka sanya soke aikin Hajjin ba. Wata annoba daga Indiya ta afka wa birnin Makka a 1831 inda ta kashe kashi uku cikin hudu na mahajjata a wurin, wadanda suka jure wa wahalhalun tafiya cikin kasashe da hanyoyi masu matukar hadari na tsawon makonni domin kawai su kai ga gudanar da aikin Hajji.

5. 1837-1858: Faruwar annoba iri-iri a jere

A cikin kusan shekara 20, an dakatar da aikin Hajji sau uku, wanda ya haifar da da mahajjata ba sa iya zuwa Makka na tsawon shekara bakwai.

A cikin shekarar 1837, wata annoba ta sake bulla a birnin Makka mai tsarki, inda ta tsayar da komi ciki har zuwa shekarar 1840.

Sannan a cikin shekarar 1846 wata mummunar cutar kwalara ta afka wa birnin Makka, da ta kashe mutum sama da 15,000, inda ta ci gaba da addabar mazauna birnin har zuwa 1850. Annobar ta sake barkewa a shekarar 1865 da kuma 1883.

A shekarar 1858, wata annobar kwalarar da ta gallabi duniya ta shiga birnin Makka, wanda hakan ya sa mahajjatan Masar suka gudu gaba daya zuwa gabar tekun Bahar Maliya na, inda aka killace su a wajen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel