Yan Majalisar Tarayya na neman kafa dokar daure masu zanga-zanga shekara 5

Yan Majalisar Tarayya na neman kafa dokar daure masu zanga-zanga shekara 5

  • Kudirin wanda aka gabatar a gaban zauren Majalisar a ranar Alhamis, ya samu amincewar majalisar domin yi masa karatu karo na biyu.
  • Kudurin dokar ya tanadar da haramta taruwar jama’a daga uku zuwa sama da niyyar tada zaune tsaye
  • Wani Dan Majalisar Dokoki dan Jam’iyyar PDP daga Jihar Imo ne ya gabatar da Kudurin Dokar

Wani Kudirin Dokar da ke bukatar yanke hukuncin daurin shekara biyar ga masu zanga-zangar da ta saba wa doka a kasar nan ya samu tsallake karatun farko a zauren Majalisar Wakilai.

Kudirin Dokar mai taken: 'Dokar Da Za Ta Sauya Dokar Laifuka ta CAP 38, a Dokokin Tarayyar Najeriya, na shekarar 2004 Don Ci Gaba Da kiyaye da Tsare Rayuwar Dan Adam da Kadarorinsa da kuma Tanadi na Musamman Kan Aikace-aikacen Gungun Mabarnata, da Samar Da Hukunci Da Sauran Abubuwa', wanda Dan Majalisa Emeka Chinedu Martins na Jam’iyyar PDP daga Jihar Imo ya dauki nauyin gabatar da shi.

Kudurin Dokar wanda aka gabatar a gaban zauren Majalisar a ranar Alhamis, ya samu salahewar Zauren Majalisar domin a yi masa karatu karo na biyu, rahoton SaharaReporters.

Abubuwan da Kudurin Dokar da aka gabatar suka kunsa, sune kamar haka: (1) Tanadin da ke cikin Dokar Aikata Miyagun Laifuka, (a cikin wannan Dokar da ake kira "Babban Sadarar Doka") wanda aka yi wa kwaskwarima kamar yadda aka bayyana a cikin wannan Kudurin Dokar (2) da za ta maye gurbin sashe na 69 na Babban Dokar, sabon sashe na 69.

DUBA NAN: Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed

Yan Majalisar Tarayya na neman kafa dokar daure masu zanga-zanga shekara 5
Yan Majalisar Tarayya na neman kafa dokar daure masu zanga-zanga shekara 5 Hoto: @NGRSenate
Asali: UGC

KU KARANTA: Za'a fita duba watan Zhul-Hajji ranar Juma'a a kasar Saudiyya

“Fassarar Kudurin:

Haramtaccen taro da Tada zaune Tsaye da Hada Gungun Masu Zanga-zanga
(a) Lokacin da mutum uku ko sama da haka suka taru da niyyar aiwatar da wata manufa ta gama gari, suka taru a irin wannan hanyar ko kuma, yayin da suka taru, suka gudanar da ayyukansu ta hanyar haddasa wa ko jefa wa mutanen unguwa tsoro da fargaba bisa dalilan da ke nuna cewa akwai alamun za su aikata danya ko suka taru da niyyar za su hargitsa zaman lafiya, ko kuma irin wannan taron ya zama ba tare da wani dalili ba kuma aka yi shi a wani lokacin da bai dace ba da ya harzuka wata jama’a wajen tayar da zaune tsaye, sunan taron haramtacce. Amma zai zama babu hujja sam koda kuwa a ce niyyar taruwarsu tun farko ba wai suna nufin aikata danya ba; amma yayin taron daga bisani suka aikata daya ko kuma dukkanin abin da aka ambata a sama to taron ya zama haramatacce.”

A riwayar Vanguard, kudurin dokar ya bayyana cewa:

“Taron mutum uku ko fiye da haka da suka taru da nufin kare duk wani gida daga mutanen da ke barazanar fasa shi domin kutsawa cikin gidan domin aikata laifi ko kuma ma kudurta aikata laifin a cikin gidan, wannan ba haramtaccen taro ba ne.
“(C) Lokacin da haramtaccen taron jama’a ya rikide zuwa haddasa hargitsi da barazana ga zaman lafiya, to za a kira wannan taron a zaman na tarzoma, kuma mutanen da suka tarun za a ce sun taru da zimmar tayar da tarzoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel