Rashin tsaro: Buhari ya gode wa sojoji saboda tabbatar da dunkulewar Najeriya

Rashin tsaro: Buhari ya gode wa sojoji saboda tabbatar da dunkulewar Najeriya

  • Shugaba Buhari ya jinjina wa rundunar sojin Najeriya wajen tabbatar da ci gaba da wanzuwar Najeriya a matsayin kasa guda
  • Sannan ya yaba wa jami’an sojin kan nuna kwarewa wajen gudanar da aiki inda ya jaddada himmar gwamnatinsa ta fuskar tallafa wa rundunar
  • Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, ya ce a rana mai kama ta yau ne aka harba harsashi na farko da ya zama masomin Yakin Basasar Najeriya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci hafsoshi da sojojin Najeriya da su bullo da sababbin dabaru domin samar wa da ’yan Najeriya kwarin gwiwa wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Kasar a daya gefen ya yaba wa rundunonin sojin Najeriyar saboda abin da ya kira nuna kwarewa da sanin makamar aikin da rundunar sojin take yi tare da ceto kasar daga wargajewa.

Shugaba Buhari, wanda ya bayyana hakan a ranar karshe na ranar Sojojin Najeriya na shekarar 2021 (NADCEL), wanda ya gudana a Abuja, rahoton The Sun.

Shugaban ya bayyana kudirin gwamnatinsa wajen samar da kayayyakin aiki da kula da jin dadin sojin domin inganta ayyukansu tare da samun damar aikin cikin walwala.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Ministan Tsaro, Manjo Janal Bashir Magashi a wajen taron, ya ce:

“Kun ceto Najeriya daga wargajewa kuma kun nuna kwarewa sosai a ayyukanku. Ina so in tabbatar muku da cewa wannan gwamnati da kuma jama’ar Najeriya suna matukar jin dadin sadaukarwar da kuka yi wajen kare kasarmu.
“Duk da haka, ina umartar hafsoshi da sauran jami’an sojin Najeriya da su kasance masu himma wajen bullo da sababbin dabaru da hanyoyin gamsar da zukatan ’yan Najeriya a wannan aikin da kuke yi a halin yanzu; sannan ina rokon ku da ku ci gaba da hada kai da aiki tare da sauran hukumomin tsaron kasar nan da ma kasashe aminan Najeriya da ke fuskantar irin wannan kalubalen domin bunkasa himmar da kuke nuna wa a halin yanzu. ”

DUBA NAN: Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed

Rashin tsaro: Buhari ya gode wa sojoji
Rashin tsaro: Buhari ya gode wa sojoji saboda tabbatar da dunkulewar Najeriya Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Za'a fita duba watan Zhul-Hajji ranar Juma'a a kasar Saudiyya

Babban Hafsan Soji yayi magana kan muhimmancin ranar

Tun da farko a jawabinsa, Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo Janal Farouk Yahaya, yayin da yake nuna muhimmancin ranar Rundunar Sojin, ya ce:

“Wannan rana, 6 ga watan Yuli tana da matukar muhimmanci a tarihin rundunar sojin kasa na Najeriya da ma Najeriyar kanta.
“A wannan ranar mai kamar ta yau a shekarar 1967 aka yi harbi na farko a Garkem, wani garin da ke kan iyaka a cikin Jihar Kuros Riba a yanzu, a wani abin da ya haifar da mummunan Yakin Basasa na Najeriya na tsawon wata 30.

Abubuwan da aka gabatar a yayin bukin sun hada da bayar da lambar yabo ta Ofishin Babban Hafsan Sojin Kasan ga hafsoshin soja guda 10 da wadansu kananan sojoji bakwai da kuma gabatar da sababbin motocin aiki kirar Toyota Hilux ga jami’an RSM na Helkwatar Sojojin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng