‘Ladaftar da dalibai da horo yana musu illa, sannan ba ya sanya su zama nagari’

‘Ladaftar da dalibai da horo yana musu illa, sannan ba ya sanya su zama nagari’

  • Masana kimiyya sun yi gargadi kan gana wa yara kanana ukuba a zaman hanya ce ta kara bata musu tarbiyya
  • Sun yi gargadin cewa azabtar da yara na kowane nau’i babu abin da zai haifar illa ya haddasa musu illa ne kawai
  • Sun ce yara miliyan 250 suke fuskantar gana musu ukuba a kowane wayewar garin Allah a duniya

Wata bita da aka gudanar a baya-bayan nan kan kananan yara ta bayyana cewa azabtar da yara a jikunansu ba ya inganta halayyar yaran hasali ma sai dai ya illa ta.

Binciken da wani rukunin masana kimiyya na duniya ya gudanar kuma aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ya nuna cewa azabtar da yara ta zahiri ba shi da tasiri wajen inganta halayen kananan yara.

A rahoton HealthWise Punch, asu binciken sun yi nazarci bincike 69 wadanda akasarin su daga Amurka ne inda suka bayyana cewa maimakon ma azabtarwar ta haifar da sakamako mai kyau, sai dai ma ta kara ta’azzara matsalolin halayyar yaran da samar da sakamako mara kyau zuwa wani lokaci.

A cewar masu binciken, kashi 63 na yara tsakanin shekara biyu zuwa hudu a duniya - kusan yara miliyan 250 - a koyaushe suna fuskantar azabtarwar ta jiki daga masu kula da su.

A cewar masu nazarin sun lura a kasashe 62, cewa sun haramta wannan dabi'a, wanda ake dauka a matsayin wani nau'in azabtarwa.

Masu binciken sun duba azabtarwar da shafi gana ukuba ga jiki kamar tsala bulala kadai, ba tare da yin la’akari da duk wani nau’in cin zarafin yara kananan ba.

DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya

‘Ladaftar da dalibai da horo yana musu illa
‘Ladaftar da dalibai da horo yana musu illa, sannan ba ya sanya su zama nagari’

KU DUBA: Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari

Sun sami cikakkiyar hujja daga kudurin Majalisar Dinkin Duniya wanda kwamitin kula da hakkin yara kanana wanda ya ba da shawarar kasashe su daina amfani da duk nau'in azabtar da yara kanana.

Masana kimiyyar sun gano cewa gana wa jiki azaba ba shi da alaka a samar da kyakkyawan sakamako ga yara kananan sai dai ma kara jefa yaran cikin hadarin fuskantar mummunan tashin hankali ko rashin kulawa.

Sun nuna cewa sakamako da ke tattare da azabtar da jikin mummuna ne, kamar matsalar gurbata dabi'a kan yaran ba tare da la’akari da jinsinsu walau miji ko mace ko kabilarsu ko launin fata sannan ba tare da la'akari da cikakkiyar tsarin kulawar iyaye ko na masu kulawa yaran ba.

Iya yadda ake azabtar da su, iya munin sakamakon

Har ila yau, marubutan sun samu shaidar cewa girman mummunan sakamakon da gana wa yaran ukuba ke haifar wa takan karu ne daidai gwargwadon yawan yadda ake azabtar da su.

Babbar marubuciyar rahoton wanda Farfesa ce a Ci gaban dan Adam da Kimiyyar Iyali a Jami'ar Texas da ke Austin, Elizabeth Gershoff, ta ce azabtar da jiki na sa halayen yara ya munana.

Gershoff. yace:

“Babu wata hujja da ke nuna cewa azabtar da jiki abu ne mai kyau ga yara.
"Dukkanin shaidu sun nuna cewa azabtar da jiki na cutarwa ga ci gaban yara da walwalarsu."
“Iyaye suna dukan yaransu saboda suna ganin yin hakan zai inganta halayensu.
"Wani abin takaici ma a nan kamar yadda bincikenmu ya gano da hujjoji kwarara kuma masu gamsarwa cewa azabtar da jiki ba ta inganta halayyar yara kuma a maimakon haka sai ta kara munana lamarin".

Masanan sun bada shawarar cewa azabtar da yara ba ita ce kyakkyawar hanyar dora su kan turba mai kyau inda hakan ke kara munana halayyar tasu.

Sun yi gargadin cewa azabtar da yara na kowane nau’i babu abin da zai haifar illa ya haddasa musu illa ne kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel