Bollywood: Aamir Khan da matarsa Rao sun rabu bayan shekaru 15 da aure

Bollywood: Aamir Khan da matarsa Rao sun rabu bayan shekaru 15 da aure

  • Fitaccen jarumin fina-finan Indiya Aamir Khan da matarsa Kiran Rao sun rabu bayan shekaru 15 da aure
  • Khan da Rao sun fitar da sanarwar rabuwar ne tare suna mai cewa za su cigaba da hada kai domin kula da dansu
  • Rao da Khan ba su fada ainihin abin da ya janyo rabuwar ba sai dai sun ce sun dade suna shirin rabuwar sai yanzu suka gamsu su sanar da duniya

Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Amir Khan ya sanar da cewa zai rabu da matar sa da suka shekara 15, mai shirya fim Kiran Rao, The Guardian ta ruwaito.

BBC ta ruwwaito cewa ma'auratan sun sanar da rabuwar su amma sun yarda zasu ci gaba da kula da dan su kuma zasu ci gaba da wasu ayyukan tare.

Aamir Khan da matarsa Kiran Rao
Jarumin Bollywood Aamir Khan da matarsa Kiran Rao. Hoto: Free Press Journal
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Sun ce:

"A tsawon shekara 15 din nan da muka shafe tare mun karu da ilimin rayuwa sosai, walwala da raha, kuma alakar mu ta ginu cikin aminci, girmamawa da kaunar juna."
"Yanzu muna bukatar bude sabon shafi a rayuwar mu -- amma ba a matsayin mata da miji ba, sai dai matsayin iyaye da kuma iyali ga kowannen mu."

Khan da Rao sun hadu ne lokacin daukar wani fim a shekarar 2001 kuma Rao ce mai taimakawa mai bada umarni, kuma suka yi aure a Disambar 2005.

Jarumin mai shekaru 56, wanda fim dinsa na dambe, 'Dangal' ya maida shi babban tauraro a kasar China, sun rabu da matarsa jaruma Reena Dutta a 2002.

"Mun fara shirye shiryen rabuwa wasu lokuta, amma yanzu ne muka ga dace mu zartar da wannan hukunci, na rayuwa ba a tare ba amma tare da gudanar da rayuwa yadda ta kamata," Khan da Rao suka ce.
"Zamu kasance iyayen masu kula da dan mu Azad, wanda zamu raina kuma ya tashi a hannun mu. Za kuma mu ci gaba da aikin hadin gwiwa a fim, gidauniyar Paani da sauran ayyukan da muke da sha'awa."
Khan da Rao yar shekara 47, sun godewa yan uwa da abokan arziki "wanda da babu su baza mu iya ba yanke hukunci cikin salama ba."
"Muna rokon masu fatan alheri da su yi mana fata na gari, kuma tare da fatan za su gane ba mun rabu ne har abada ba, hanya ce ta fara sabuwar rayuwa."

An yi jana'izar tauraruwan Kannywood Zainab Booth a Kano

A yau Juma'a 2 ga watan Yuli ne aka yi jana'izar tauraruwan wasan kwaikwayo na hausa, Zainab Booth, wacce ta rasu a ranar Alhamis.

Premium Times ta ruwaito cewa a birnin Kano aka birne marigayiyar wacce ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.

Daruruwan abokan aikinta da masu aiki a masana'antar fim, irin su Ali Nuhu, Falulu Dorayi da Yakubu Mohammed da masoya da dama sun hallarci jana'izar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel