El-Rufai: Ba ni da bukata a zaben 2023, shugabancin Kasa damuwa ne ga mai shekara 62

El-Rufai: Ba ni da bukata a zaben 2023, shugabancin Kasa damuwa ne ga mai shekara 62

  • Gwamna El-Rufai ya ce Shugabancin Kasa ya yi wa mai shekara 62 nauyi
  • A cewarsa rike mukamin gwamnan jiha guda kadai ya masa nauyi ballantana jihohi 36
  • Ya koka yadda sumar kansa duk ta yi furfura sakamakon nauyin kujerar gwamna

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir el-Rufai, ya bayyana cewa aikin shugabancin kasa ga mai shekara 62 wahala ce kawai.

Ya fadi hakan yayin da yake amsa tambayar cewa ko yana shirin zama Shugaban Kasa a 2023 a hira da BBC Pidgin.

Gwamnan ya ce aikinsa na gwamnan jiha guda daya rak na masa nauyi barin ma a yi maganar shugabancin Najeriya.

A cewarsa, nauyin zamansa gwamna kawai ya sanya kansa gaba daya ya yi furfura cikin shekara shida.

Yace:

“Ka dubi furfurar kaina. Idan ka dubi hotuna sanda aka rantsar da ni, sumar kaina baka kirin take lokacin; amma duba yadda ya ta zama yanzu. Aiki ne gagarumi kuma a hakan ma wai gwamna ne kawai — jiha daya cikin jihohi 36.
“Gagarumin aiki ne, kwarai; sannan mawuyaci, eh, amma wai a hakan ma ba za ka kwatanta shi da Najeriya ba. Shugabancin Najeriya ba aikin kawai ba ne, ya fi gaban mai shekara 62.

DUBA NAN: Ranar 28 ga Yuli za'a yanke hukunci kan El-Zakzaky da Maidakinsa

El-Rufai: Ba ni da bukata a zaben 2023
El-Rufai: Ba ni da bukata a zaben 2023 — Shugabancin Kasa damuwa ne ga mai shekara 62 Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: UGC

KU KARANTA: Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki

An tambaye shi ko yana da sha’awar zama mataimakin shugaban kasa, sai ya kada baki da cewa:

“Ban taba tunanin wannan ko kadan. Na fada a baya can cewa a irin tsarin siyasarmu bayan Shugaba Buhari ya kammala shekara takwas na wa’adinsa, ya kamata Shugabancin ya koma Kudanci.”

El-Rufa'i ya taya Buhari neman zabe duk da shekarunsa sun wuce 70 a lokacin

Amma idan za a tuna el-Rufai da kansa ya yi yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari wanda a lokacin yake da shekara 73 a zaben 2015.

Ya kuma yi yakin neman sake zaben Buhari wanda yake da shekara 77 a zaben 2019.

Zuwa lokacin da Shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu zai zama yana da shekara 81 — kuma shugaba mafi tsufa da ya mulki Najeriyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel