Da tsafe-tsafe nike kare kaina, makaman da aka samu a gidana sharrin gwamnati ne — Igboho

Da tsafe-tsafe nike kare kaina, makaman da aka samu a gidana sharrin gwamnati ne — Igboho

  • Igboho ya amince cewa yana amfani da tsafi da sauran siddabarun gargajiya domin kariyar jikinsa
  • Ya ikirarin cewa shi ma wani sabon Ken Saro Wiwa ne
  • Sannan ya shawarci Shugaba Buhari da ya koyi darasi daga abin da ya faru a baya

Mutumin nan mai ikirarin kare hakkokin ‘yan kabilar Yarbawa wato Sunday Adeyemo Igboho ya yi martani kan dirar mikiya da jami’an tsaron sirri na DSS suka yi a gidansa ranar Laraba da daddare.

Yace dole ne na fayyace wa duniya gaskiyar lamarin da ya faru sakamakon samamen da jami’an tsaron sirri na DSS suka kai a gidansa da daren Alhamis.

A cewarsa. sun kutsa cikin gidan ba tare da samun izinin yin hakan daga kotu ko kuma a gayyacesa domin yin bayani ba, rahoton Vanguard.

DUBA NAN: Ranar 28 ga Yuli za'a yanke hukunci kan El-Zakzaky da Maidakinsa

Da tsafe-tsafe nike kare kaina, makaman da aka samu a gidana sharrin gwamnati ne — Igboho
Da tsafe-tsafe nike kare kaina, makaman da aka samu a gidana sharrin gwamnati ne — Igboho
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da jarin N50,000 na fara kasuwanci - Babban Biloniya ya bayyana yadda yayi arziki

Yace:

“Jami’an sun kutsa cikin gidana inda suka lalata kayayyakin gidan sannan suka kashe wadansu mutane tare da sace muhimman ababuwa da kudade. Kamar yadda duniya ta shaida a hotuna da faifan bidiyon da suka fitar.
“Mutanen Najeriya da duniya duk sun shaida yadda nake turjiya wa kashe-kashe da fyade da sace mutane da Fulani makiyaya ke aikatawa kan al’ummata a yankin Kudu maso Yamma.
“Gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen taka birki ga makiyayan ‘yan ina da kisa ne ya saka dole in bada gudumawata.
“Idan da a ce gwamnatin ta yi abin da dace wajen sauke nauyinta na kare al’ummomin yankin Kudu maso Yamma da ma sauran sassan kasar daga barnar da ‘yan kabilar Shugaban Kasar (Fulani) suke aikatawa ba, to kuwa da ba abin da ya sha mini kai.

Karya suka min, ba makamai na bane

Ya kara da cewa ya kamata ‘yan Najeriya da ma duniya su sani cewa makaman da jami’an tsaron suka nuna wa kafofin yada labarai cewa sun samo a cikin gidansa ko dai sune suka shigar da su cikin gidana ko kuma sun fito da su daga rumbun ajiyar makamansu kawai domin su bata masa suna sannan su yi masa sharri.

Yace

“Wadannan makaman ba nawa ba ne, sharri ne kawai irin na gwamnati. Ina kare kaina da tsafe-tsafe da ma siddabaru irin na gargajiya, amma ba wai da bindiga ba.
“Gwamnatin Tarayya ta mini sharri. Sannan lura da yadda lamarin ya wakana gaskiya ta yi halinta. Me dalilin da jami’an tsaro za su kai samame gidana da talatainin dare inda suka fara lalata kyamarorin da ke daukar bayanai na gidan kafin su fara aika-aikarsu, idan dai ba wai suna da wata manakisa ba?

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng