Dalibin Najeriya ya kera mota a zaman aikin kammala karatunsa, an nuno shi yana gwajin tuka ta

Dalibin Najeriya ya kera mota a zaman aikin kammala karatunsa, an nuno shi yana gwajin tuka ta

  • ’Yan Najeriya na jinjina wa dalibin Jami’ar Fasaha ta Minna wanda ya kera mota a zaman aikin kare karatunsa a jami’ar
  • Wani bidiyo da ya yadu ya nuno wani kamar motar gaske yana daukar fasinja da direba lokacin da suke daf da gwajin tuka motar
  • Da dama daga cikin wadanda suka yi tsokaci kan bidiyon sun ce matasan Najeriya na bukatar a ba su damar baje fasaharsu

Babu karya game da batun cewa akwai ’yan Najeriya da dama Allah Ya ba su fasaha.

Akwai misalai da dama da suke nuni da hakan. Ko kun tuna Jerry Issac Mallo wanda ya kera mota a shekarar 2019?

Wani faifan bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta wanda Instablog9ja ya wallafa a shafinsa na Instagram ya yi ikirarin wani dalibi dan Najeriya daga Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna ya kera mota a matsayin aikinsa na karshe domin kammala karatun jami’a da aka fi sani da Final Year Project.

DUBA NAN: Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi

Dalibin Najeriya ya kera mota
Dalibin Najeriya ya kera mota a zaman aikin kammala karatunsa, an nuno shi yana gwajin tuka ta Hoto: Instablog9ja
Asali: Instagram

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Babban Aikin Kammala Karatun Jami’a

An jiyo wata murya a faifan bidiyon tana tambayar mutumin ko dai wannan aikin kammala karatunsa na jami’a ne.

Daga bisani ya ce za a aika bidiyon zuwa shafin Instagram domin yada shi ga jama’a. A cikin bidiyon an ji an rada wa motar suna Merczy. Gaban motar yana da fadin gaske kamar da Escalade.

Mutane sun kalli bidiyon motar cike da mamaki.

Mutane da dama sun tsaya suna kallon kirkirar motar sanda matashin tare da fasinjansan suka shiga suka zauna a cikin motar suna kokarin yin gwajin tuka ta.

Koda yake ya kamata a fahimta cewa kafar yada labarai ta Legit.ng ba ta iya tantance sahihancin faifan bidiyon ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton inda ya samu fiye da mutum 132,000 suka kalle shi, da alama dai faifan bidiyon ya samu tagomashi sosai a intanet.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng