Bidiyon Dala: Ganduje ya nemi janye karar da ya shigar kan Jaafar Jaafar

Bidiyon Dala: Ganduje ya nemi janye karar da ya shigar kan Jaafar Jaafar

  • Lauyoyin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun shigar da bukatar neman janye karar da suke yi wa dan jarida Jaafar Jaafar a ranar Litinin
  • Dan jaridar kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian ya nemi mafakar siyasa a Birtaniya kwanakin da suka wuce saboda zargin ana barazana kan rayuwarsa
  • Kotun ta ce sai ranar 6 ga watan gobe za ta saurari bukatar janye karar

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci janye karar da ya shigar kan dan jaridar nan kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian (da ake wallafa wa a intanet) Jaafar Jaafar, Solacebase ta ruwaito.

Ganduje ya kai karar Jaafar zuwa kotu tun a shekarar 2018 kan wani labarin da Daily Nigerian ta wallafa mai taken: BABBAN LABARINMU: AN GANO WANI GWAMNAN NAJERIYA YANA KARBAR HANCIN $5M, da ma wasu labaran da suka biyo baya da shafin jaridar ya wallafa kan labarin wanda gwamnan ya ce sun bata masa suna.

Daga nan gwamnan, ya bukaci kotun da ta bayyana cewa “aikin bugawa da yada kalaman batanci, faifayin bidiyo na karya a kafar yada labaran ta yanar gizo, hari ne kuma bata sunan da cin mutuncin mai shigar da karar ne wanda ake karar ya aikata. ”

Idan za a iya tunawa mawallafin jaridar ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya koma Ingila da zama sakamakon zargin ana yiwa rayuwarsa barazana.

Biyo bayan sababbin barazana, ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, za a dora wa laifi muddin dai wani abu ya same shi sakamakon wallafa faifan bidiyon da ake zargin gwamnan na sanya Daloli a aljihun babbar rigarsa.

DUBA NAN: Najeriya ce kan gaba a yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Sahara - Ministan Ilimi

Bidiyon Dala: Ganduje ya janye shigar kan Jaafar Jaafar kotu
Bidiyon Dala: Ganduje ya nemi janye karar da ya shigar kan Jaafar Jaafar
Asali: Twitter

DUBA NAN: Ina PDP, ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara

Sai dai a cikin wata takarda zuwa ga Babbar Kotun Jihar Kano mai dauke da kwanan watan ranar 28 ga Yunin 2021, lauyoyin Ganduje, karkashin jagorancin Cif E.O.B Offiong, SAN, sun gabatar wadannan bukatun a gaban kotun kamar haka:

Umarnin a bayar da izini ga Mai shigar da kara wajen dakatar da da'awar da yake yi a kan Kara mai lamba ta K/519/2018 a kan wanda ake tuhuma a gaban wannan Kotun Mai Daraja.

An ajiye sai ranar 6 ga watan Yulin 2021 za a saurari bukatar da lauyoyin Gandujen suka shigar.

Legit ta tattauna da makusancin Jafar

Legit ta tuntubi daya daga cikin ma'aikatan Jafar Jafar, Ibrahim Ramalan, kuma ya tabbatar da wannan labari.

Yace lallai sun samu labarin janye karar.

Da muka tambayesa shin Jafar zai dawo Najeriya kenan, yace ba'a sani ba tukun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng