Zaben 2023: Dalilan Da Suka Sanya Gwamna Bala Ya Dace Da Zama Shugaban Kasa, Daga Danlami Babantakko

Zaben 2023: Dalilan Da Suka Sanya Gwamna Bala Ya Dace Da Zama Shugaban Kasa, Daga Danlami Babantakko

Danlami Babantakko , ya rubuto wannan ra'ayi ne daga jihar Bauchi yayinda ake sauraron gwamnan jihar ya bayyana ra'ayinsa kan takarar zaben shugaban kasa a 2023.

Nan da kwanaki kadan Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi zai bayyana matsayar sa kan ko zai fito takarar shugaban kasa a zaben 2023 ko akasin haka. Wannan ya biyo bayan bukatar ya fito takarar da wata kungiyar matasan Arewa LYLF ta yi.

Idan ka bibiyi rayuwarsa musamman ta fannin siyasarsa, Gwamna Bala mutum ne da a koda yaushe ake ganin ya fi cancanta da jagoranci a cikin jagorori.

Sanata Bala Muhammad, tsohon dan jarida ne, inda ya shafe tsawon shekaru ana gungurawa da shi a harkar.

Tsohon edita ne da rusasshiyar jaridar 'The Mirage' a shekarar 1982 - 1983, sannan tsohon mai aika rahotanni ne ga kamfanin dillacin labaran Nijeriya NAN.

Ya yi aiki da tsohuwar jaridar The Democrat, 1983 -1984, sannan ya yi aiki da ma'aikatar cikin gida ta Nijeriya tsakanin shekarun 1984 - 1994.

Kauran Bauchi ya taba zama babban jami'in shigo da kayayyaki a ma'aikatar albarkatun kasa ta Najeriya tsakanin 1995 - 1997, kazalika ya taba zama mataimakin darakta a ma'aikatar wuta ta Najeriya tsakanin 1997 - 1999

A shekarar 2003 ne ya zama daraktan gudanarwa na hukumar sufurin jiragen ruwa ta Najeriya.

Daga bisani ne kuma ya yi ritaya daga aikin gwamnati a kashin kansa ya kuma tsunduma siyasa.

Ya yi Sanata, ya rike mukamin ministan Abuja, inda yanzu haka Gwamna ne mai ci.

DUBA NAN: Kotun Abuja ta sanar da ranar da za a sake gurfanar da tsohon gwamna, Orji Uzor Kalu

Dalilan Da Suka Sanya Gwamna Bala Ya Dace Da Zama Shugaban Kasa
Zaben 2023: Dalilan Da Suka Sanya Gwamna Bala Ya Dace Da Zama Shugaban Kasa, Daga Danlami Babantakko
Asali: Original

DUBA NAN: An nada Alkalan Shari'a 34 a jihar Kano bayan gwaji

Duk wanda yake da irin wannan tarihi a gwamnatance kuma a siyasance abin a rike shi hannu bibiyu ne. Duk da dai cewa kungiyar ta NYLF ta kawo dalilanta na neman Gwamna Bala ya fito takarar shugaban kasa a 2023. Amma akwai tarin hujjoji da dama da suka sanya Gwamnan ya cancanci takarar shugaban kasa.

A yanzu haka Gwamna Bala yana daga cikin hazikan gwamnonin da suka taka rawar gani a kasar nan. Ya gudanar da ayyukan cigaba masu tarin yawa, wanda hakan ya sa ake ganin ba a yi Gwamna kamar sa ba a tarihin jihar Bauchi.

Zuwa yanzu Gwamna Bala ya aiwatar da aikin manya da kananan tituna a cikin jihar Bauchi da sauran kananan hukumomin jihar, ya kuma kawo cigaba a harkar ilmi, ta hanyar gina sabbin makarantu tare da sabunta wasu da dama. A fannin harkar lafiya da bunkasa tattalin arziki ma ya yi matukar taka rawar gani.

Ita ma kanta jam'iyyar PDP tana da muradin ganin Gwamna Bala ya zama dan takarar ta a matakin shugaban kasa a zaben 2023. Saboda PDP ta gano cewa tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar ta ya zama tsohon yayi, wanda ya kamata a baiwa sabbin jini dama wadanda za su karbu a wurin al'ummar Nijeriya.

Yanzu 'yan Nijeriya sun soma gajiya da cigaba da tsayar da Atiku Abubakar takara a matakin sama, domin nan gaba kadan za su soma zargin akwai wani abu a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng