Azonto: Gwamnatin Benue ta rushe gidajen kasurgumin mai garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo
- Yan sanda sun rushe wasu gine-gine biyu mallakin wani dan ta'adda da suke nema ruwa a jallo
- Yan sandan sun kuma kama mutum biyu tare da makudan kudade hade da makamai
- CSP Justin Gberindyer ne ya jagoranci atisayen kuma ya ce sunyi nasara sosai
Gwamnatin Jihar Benue a ranar Litinin ta rushe wasu gidaje biyu da ake zargi mallakin Cephas Aondofa Shekere, da aka fi sani da 'Azonto' ne, kuma wanda aka nema a jihar bisa zargin ta'addanci da garkuwa da mutane.
Daily Trust ta ruwaito cewa gine-ginen suna wurare daban-daban a Makurdi.
Azonto wanda ya karbi shugabancin daga tsohon dan ta'adda, Terwase Akwaza da ake kira 'Gana' bayan da sojoji suka kawar da shi a watan Satumbar bara lokacin da yake dawowa daga Katsina-Ala zuwa Makurdi, rahoton The Punch.
DUBA WANNAN: An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina
Sai dai, rushewar da akayi an yi ne bisa dokar hana garkuwa da mutane, wanda ta bayyana abubuwa da dama ciki har da rushe duk wajen da mutum ya mallaka wanda dasu ake ayyukan ta'addanci.
Wannan na zuwa ne bayan yan sanda sun kama mutum biyu daga tawagar yan bindigar wanda suka tabbatar su suka addabi mutanen Sankera, Logo, Ukum da Katsina-Ala na jihar.
Wani samame da CSP Justin Gberindyer ya jagoranta na 'Operation Ozenda' ya yi sanadin kama mutum biyu wanda aka gano makudan kudade.
Yan sandan sun kuma kama harsashi 30 na bindigar AK47 a wuraren da suka rushe bayan taron jami'an tsaro su kuma suna kulla mugun aikin su.
Mutum biyun da ake zargi ne suka jagoranci yan sanda zuwa gidajen sun tabbatar su yaran uban daba, Azonto, wanda yan sanda ke nema ruwa a jallo a Benue.
KU KARANTA: Mutum ɗaya ya mutu, da dama sun jikkata a harin da 'dodo' ya kai wa masallata a Osun
Daya a cikin wanda ake zargin, ita ce uwar gidan Azonto sai kuma dayan, mai suna, Steven Tor-Ikyo, wanda aka kama da miliyoyin kudi da za a siyo makamai.
Abin da 'yan sanda suka ce
CSP Gberindyer, wanda ya zanta da yan jarida a wajen rushe wuraren yace wanda ake zargin sun amsa laifin su kuma sun tabbatar Azonto suke wa aiki.
Dan sandan ya ce wanda ake zargin, Steven shi yake taimakawa Azonto siyan kayayyaki a Abuja, Port Harcourt, Lagos da Makurdi.
Saboda haka mun rushe gidajen Azonto wanda shi (Steven) ya taimaka aka gina bayan an same su cikin garin Makurdi.
Asali: Legit.ng