Jerin kasashen Afirka 10 da aka fi samun zaman lafiya da akasin hakan

Jerin kasashen Afirka 10 da aka fi samun zaman lafiya da akasin hakan

Kasar Mauritius ta zama kasa mafi zaman lafiya a yankin sub saharan Afirka a cewar wani rahoto da Global Peace Index ta wallafa a shaekarar 2021.

Shugabannin kasashen Afirka
Shugabannin kasashen Afirka. Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Buhari ya yi martani kan barazanar da Niger Delta Avengers ta yi na gurgunta tattalin arzikin Nigeria

Rahoton wanda cibiyar tattalin arziki da zaman lafiya ta wallafa ya nuna cewa kasar Ghana ce ta biyu a cikin jerin kasashen da suka fi zaman lafiya a nahiyar Afirka.

An yi kididdigan kasashe 44 a yankin Afirka sannan a kididigan kasashen duniya 163, kasar Iceland ce ta zama mafi zaman lafiya a duniya.

Afganistan ce kasa mafi karancin zaman lafiya a duniya a cewar rahoton. Nigeria ce ta zo na 146 cikin jerin kasashen duniya 163 da aka yi nazarin a kansu.

IEP ta yi la'akari da abubuwa kamar tsaftaccen siyasa, zanga-zanga, muggan laifuka, safarar makamai, rikicin cikin gida da sauransu ne wurin yin kididdigar.

Ga jerin kasashen Afrika 10 da aka fi zaman lafiya a 2021

1. Mauritius

2. Ghana

3. Botswana

4. Sierra Leone

5. The Gambia

6. Senegal

7. Tanzania

8. Malawi

9. Equatorial Guinea

10. Namibia

KU KARANTA: An kama garada 3 da suka ɗirka wa matar aure ciki kafin shigar da ita 'Ɗarikar Haƙiƙa' a Katsina

Kasashe 10 da ke kan gaba wurin rashin zaman lafiya a Afirka

1. South Sudan

2. Somalia

3. The Democratic Republic of the Congo

4. The Central African Republic

5. Mali

6. Nigeria

7. Cameroon

8. Ethiopia

9. Niger

10. Eritrea

Legas na cikin birane 10 mafi wahalar zama a duniya a shekarar 2021

An sanya Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya a matsayin birni na biyu mafi wahalar zama a duniya, bisa ga alkaluman birane mafi sauki da mafi gajiyarwa na 2021 wanda VAAY.com ta fitar.

Kididdigar ta tsara biranen 100 ta hanyar lura da abubuwa kamar aminci da tsaro, kwanciyar hankali na siyasa da zamantakewa, yawan jama'a, iska, hasken wuta, da matakan hayaniya, yawan cunkoson ababen hawa da yanayin gari don ƙayyade matakan gajiyarwar.

Sauran abubuwan da aka yi la’akari da su sun hada da yawan rashin aikin yi, shugabanci, da kuma lafiyar kwakwalwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel