Majalisar Dattawa ta jefi NPA, Hadimin Buhari da zargin tafka badakalar Biliyoyin kudi

Majalisar Dattawa ta jefi NPA, Hadimin Buhari da zargin tafka badakalar Biliyoyin kudi

  • Sanatoci sun yi bincike kan wasu kudin tsarin PICOMSS da ke asusun NPA
  • Kwamitin Majalisa ya ce an dauki wadannan kudi, an kai zuwa asusun NSA
  • Sanata Matthew Urhoghide ya bayyana sakamakon binciken da ya gudanar

Majalisar dattawa ta kasa ta cusa ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro na NSA, a wani zargin tafka badakalar makudan kudi.

Jaridar This Day ta ce ana zargin ofishin mai ba shugaban kasar shawara game da sha’anin tsaron da karkatar da kudi har N1, 075, 266, 599.06.

Haka zalika ana zargin wannan ofis da karkatar da $2,301,329.54 da kuma €196,257.42 daga hukumar NPA mai kula da tashoshin ruwan Najeriya.

KU KARANTA: Alakarmu da Dangote a hukumar NPA - Hadiza Bala Usman

An sulale da kudin aikin PICOMSS zuwa asusun NSA

Idan aka yi lissafin jimillar wadannan kudi a darajar Naira ta gida, sun haura Naira biliyan biyu.

Ana zargin NPA da karkatar da wasu kudi wanda aka ware wa kwamitin shugaban kasa na horas da ma’aikatan da ke aiki a kan ruwa watau PICOMSS.

Rahoton ya ce kwamitin majalisar dattawa da ke kula da baitul-mali ya ce an wawuri wadannan kudi, an jefa su zuwa wani asusun NSA a shekarar 2017.

Jaridar Independent ta tabbatar da wannan lamari, ta ce amma sai da aka samu amincewar majalisar zartarwa ta kasa kafin a dauki wadannan kudi.

KU KARANTA: Sanatoci za su fallasa MDAs da ke lakume Ƙudin Gwamnati

Majalisar Dattawa
'Yan Majalisar Dattawa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kwamitin binciken Sanata Matthew Urhoghide

Shugaban kwamitin, Sanata Matthew Urhoghide, ya yi wannan bayani yayin da yake gabatar da rahoton bincikensu ranar Talata, 23 ga watan Yuni, 2021.

Sanatan ya ce NPA ta karbi cikon kudin PICCOMS da ake tara wa daga 2008 zuwa 2013, wanda sun hada da N238,948,138.12, $238,540.80 da kuma €168, 220.64.

Urhoghide ya ce babu abin da ke nuna an yi amfani da kudin wajen horas da ma’aikata kamar yadda aka bada umarni, sai da aka kai kudin wani asusun.

A karshe kwamitin ya bukaci NPA ta karbo N1,314,214,737.18, $2,539,870.34 da €364,478.06 a asusun NSA, ta maida su cikin baitul-malin gwamnatin kasa.

Dazu ne aka ji shugaban kamfanin NNPC na kasa, Mele Kolo Kyari, ya bayyana ainihin farashin da ya kamata a rika saida litar fetur a gidajen mai a Najeriya.

Mele Kyari ya ce tsakanin N140bn zuwa N150bn ake kashewa duk wata a matsayin tallafi domin ka da kudin mai ya tashi, har gobe ana saida fetur ne a N162.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng