Kwarto ya diro ta 'taga' daga bene hawa biyu yayin da maigida ya dawo (Hotuna)

Kwarto ya diro ta 'taga' daga bene hawa biyu yayin da maigida ya dawo (Hotuna)

Rabon wahala ne ya ja wani mutum ya fado daga taga mai nisan taku 20 daga kasa kuma sanye da kamfai da safa. Hakan ya faru ne kuwa bayan da mijin masoyiyar shi ya dawo gida da wuri ba lokacin da ya saba ba.

An dauki bidiyon ne a kasar Switzerland yadda katon mutumin ke saukowa a gaggauce daga hawa na biyu na bene.

Kwarto ya diro ta 'taga' daga bene hawa biyu yayin da maigida ya dawo (Hotuna)
Kwarto ya diro ta 'taga' daga bene hawa biyu yayin da maigida ya dawo (Hotuna)
Asali: Twitter

A bidiyon an ga mutumin na gaggawar kama wani sashi na tagar don gudun muguwar faduwa da kuma tozarcin da zai iya samu.

Amma kuma, cikin dakiku kadan komai ya kubuce masa inda ya fado cikin wata motar bola da ke ajiye. Hakan yasa yayi dumu-dumu cikin dattin.

DUBA WANNAN: Biyafara: Trump ya gayyaci Kanu taron gangamin yakin neman zabensa a Amurka

Bayan da ya fado cikin wannan dattin, an ji muryar matar da ke daukar wannan bidiyon na cewa "wayyo Allah na" da harshen Jamus.

Kwarto ya diro ta 'taga' daga bene hawa biyu yayin da maigida ya dawo (Hotuna)
Kwarto ya diro ta 'taga' daga bene hawa biyu yayin da maigida ya dawo (Hotuna)
Asali: Twitter

Bayan fadowa ta kan cikin shi a bayan motar, ya gangara zuwa mazaunin direba.

Jami'an tsaro na Zurich Cantonal sun tabbatar da aukuwar lamarin. Sun ce ya faru ne a Wallisellen amma ba zasu saki karin bayani a kan hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel