Rikicin cikin gida ya yi kamari, ‘Ya ‘yan Jam’iyya 20000 sun sauya-sheka daga APC a rana 1

Rikicin cikin gida ya yi kamari, ‘Ya ‘yan Jam’iyya 20000 sun sauya-sheka daga APC a rana 1

Mutane kimanin 20, 000 suka bar Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Kwara

Abdulfatai Abdulrahman ya jagoranci ficewar fusatattun ‘Ya ‘yan jam’iyyar

Kawo yanzu tsofaffin ‘Ya ‘yan APC ba za su fadi jam’iyyar da za su shiga ba

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Asabar cewa wasu dubunnan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki sun sauya-sheka a garin Ilorin, jihar Kwara.

Fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyyar sun kafa wata tafiya ta dabam bayan an dauki lokaci ana rikici.

Shugaban APC na yankin jihar Kwara ta tsakiya, Alhaji Abdulfatai Abdulrahman, ya jagoranci wasu manyan jam’iyya, suka tabbatar da ficewarsu jiya.

KU KARANTA: 'Dan takarar gwamnan APC a Kwara ya sha da kyar a wajen kamfe

Alhaji Abdulfatai Abdulrahman ya ce nan gaba za su bayyana sabuwar jam’iyyar da za su kafa.

Abin da ya sa su mu ka bar APC

“Abin kunya ne, abin takaici ace jam’iyyar APC ta gagara amfana da nasarar da aka samu a jihar Kwara a lokacin da ta ke tsakiyar mulki.” Inji Abdulrahman.

“Burin mutanen jam’iyya na cin moriyar guminsu bai kai ga ci ba saboda rikicin gaira babu dalili da aka kawo. Ba abin da mutanen Kwara suka zaba ba kenan.”

Abdulrahman ya ce wadanda su ka bar APC za su kai 20, 000, ya ce daga ciki akwai shugabannin jam’iyya na mazabu da jagororin mata da matasa na fadin jihar.

KU KARANTA: APC ta rasa kujerar Majalisa a Kwara a hukuncin kotu

Rikicin cikin gidan APC
Ana kona tsintsiya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hakan na zuwa ne a lokacin da aka fara buga gangunan siyasar 2023 a jihar Kwara. Kafin yanzu an dade ana samun rikici tsakanin manyan jiga-jigan jam'iyya.

The Nation ta ce an yi wannan gangami ne a dakin taro na MM Event centre venue da ke kan titin Offa Road, a Ilorin, inda ‘ya ‘yan APC suka kona tulin tsintsiyoyinsu.

Daga cikin tsofaffin magoya bayan na APC, an ga wasu dauke da tambarin jam’iyyar YPP. Ana zargin yaran tsohon ‘dan takarar gwamna, Alhaji Yakubu Gobir ne.

A baya kun ji yadda aka yi wa shugaban rikon kwaryan APC na jihar Kwara, Hon. Bashir Bolarinwa da mutanensa ‘dan karen duka a taron da ya koma rigima.

Bashir Bolarinwa ya ce lamarin ya faru ne bayan an kira su zuwa wajen rajistar da kwamitin APC na Sanata John Danboyi ta ke yi, sai aka yi masu shigo-shigo-ba-zurfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel