Mutum 3 sun mutu, 13 sun jikkata sakamakon fashewar tankan mai a Legas

Mutum 3 sun mutu, 13 sun jikkata sakamakon fashewar tankan mai a Legas

  • Mutum 3 sun rasu sannan wasu mutanen 13 sun samu rauni bayan fashewar tankar mai a Legas
  • Hukumar bada agaji na kasa NEMA da hukumar bada taimakon gaggawa na jihar Legas sun tabbatar da afkuwar lamarin
  • LASEMA ta kuma ce gobarar ya yi sanadin konewar wasu motocci 22 da aka yi fakin dinsu a wani wuri kusa da inda gobarar ya tashi

Mutane uku sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 13 suka jikkata sakamakon fashewa da tankar man fetur ta yi a Legas a daren ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito.

Premium Times ta ruwaito cewa tankar ta fashe na a Mobolaji Anthony Way, kusa da Opic Plaza da Shereton Hotel a Ikeja, Legas.

Gobarar tankar mai a Legas
Gobarar tankar mai a Legas. Hoto: News Wire
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan bindigan da suka kai hari Makarantar Kebbi sun harbi ɗalibai biyu, Shaida

Jami'an bada taimakon gaggawa sun isa wurin domin bada tallafi ga wadanda abin ya shafa bayan an sanarwa da su afkuwar lamarin.

Abin da hukumomin bada agaji suka ce

Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas, LASEMA, ta ce fashewar tankan ya shafi OPIC Plaza, inda ya yi sanadin konewar motocci 22 da aka ajiye a harabar wurin.

Shugaban LASEMA, ya ce mutanen da suka iso wurin da farko sun kawar da wasu motocci da kayayyaki da ke kusa da wurin domin kada gobarar ta shafe su.

Hukumar bada agajin gaggawa na kasa, NEMA, ta tabbatar da rasuwar mutum uku da aka gano gawarsu a ranar Jumma'a.

KU KARANTA: 'Yan bindigan da suka kai hari Makarantar Kebbi sun harbi ɗalibai biyu, Shaida

Da farko, LASEMA ta bada rahoton cewa ta ceto mutum 13.

Hukumar ta ce maza tara da mata hudu da suka jikkata sakamakon gobarar sun samu taimakon farko kafin daga bisani aka garzaya da su asibitoci a Legas.

An kawar da tankar da ta janyo gobarar, sannan an rufe wurin domin cigaba da bincike game da afkuwar lamarin.

A wani rahoton, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Talata, ya amince da dakatar da ayyukan Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na jihar Zamfara (ZAROTA) bayan yawan koke da ake yi da ayyukan jami'an hukumar, Daily Trust ta ruwaito.

TVC News ta ruwaito cewa daga yanzu rundunar hadin gwiwa ta yan sanda, VIO, FRSC da jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ne za su rika sa ido kan ayyukan ZAROTA, a cewar sakataren dindindin na ayyukan fadar gwamnati, Yakubu Haidara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel