Jami'an tsaro na yiwa matasanmu kisan gilla, Dattawan Igbo

Jami'an tsaro na yiwa matasanmu kisan gilla, Dattawan Igbo

  • A ranar juma'an data gaba tane Dattawan alu'mmar ibo suka bayyana cewa hukumomin tsaro na dauki dai-dai ma matasan su
  • Shugaban Kungiyar wanda yake tsohon gwamnan jihar Anambra Chukwuemeka Eziefe ya sanar da haka a wani taron manema labarai da ya gudana a garin Abuja
  • Suna shiga gidajen mutane ba bisa ka'ida ba,suna kama maza tare da kashe matasan da basu ji ba basu gani ba, yace

Shugaban kungiyar dattawa Igbo, kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Cif Chukwuemeka Ezeife, ya ce matasa da dama, akasarinsu maza, ana kashe su ba bisa ka'ida ba a kowace rana daga jami'an tsaro a yankin.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, rahoton ChannelsTV.

Yace:

"Mun yi Allah wadai ba tare da wata damuwa ba game da barnata dukiyar jama'a a yankin Kudu maso Gabas, saboda ba halinmu ba ne kone-kone, da neman fitina" .
“Mun yi imanin cewa ba daidai ba ne kawai a yi amfani da makami wurin kashe wanda bai jiba bai gani ba
“A yanzu haka hukumomin tsaro sun mamaye gidajen mutane ba bisa tsari ba a lokutan da bai kamata ba wurin kamo mambobin IPOB da mambobin kungiyar ESN.
“Suna kame maza kuma wasu lokuta suna harbin matasa da basu ji ba basu gani ba.
Don haka muna kira ga Shugaba Muhamamdu Buhari, Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai, Tarayyar Afirka, ECOWAS, da su dauki matakin gaggawa don dakatar da kisan kare dangin da ake yi wa ’yan kabilar Ibo a halin yanzu a Kudu-maso-Gabas da wasu sassan Kudu-maso-Kudu.”

KU DUBA: A shirya kuri’ar raba gardama, a taimaka wa Ibo su balle daga Najeriya: Kungiyoyin Arewa

Jami'an tsaro na yiwa matasanmu kisan gilla, Dattawan Igbo
Jami'an tsaro na yiwa matasanmu kisan gilla, Dattawan Igbo Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya ciwo bashin fiye da biliyan 10 a kowace rana cikin shekara shida na mulkinsa

Yaren da suka fi fahimta ’

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi barazanar tunkarar IPOB "a yaren da suke fahimta", kalaman da ya haifar da martani daga fusatattun 'yan Najeriya da dama yayin da take alakanta ta da yakin basasa da Najeriya ta zubar da jini.

Rayukan al'ummar ibo da dama sun salwanta yayin yakin basasa.

Duk da haka,gwamnatin Muhammadu Buhari ta ninka kudurin ta na kai wa ‘yan kungiyar IPOB hari, wadanda aka sanya su a matsayin‘ yan ta’adda.

IPOB na yin kira ga ballewar wani yanki na yankin kudancin kasar don samar da Jamhuriyar Biafra.

Lokacin da Shugaban kasar ya ce za a bi su‘da yare da suka fi fahimta,’ sai ya sake cewa za a hadu da karfi da karfe wajen amsa ga ayyukan tsaro a duk duniya.

“Wannan ba nuna kiyayya ba ne, alkawari ne na kare‘ yan cin yan kasa daga cutuwa. Ba bu yanda za a ace gwamnatin ta zuba ido ga‘yan ta’adda, Yace.

A bangare guda, gamayyar kungiyoyin Arewa sun bukaci Majalisar Tarayya da ta ayyana dokar wajibci ta hanyar shirya kuri’ar raba gardama domin bai wa al’ummar yankin Kudu maso Gabas damar kada kuri’ar ko dai su ci gaba da zama a Najeriya ko akasin haka.

Gamayyar ta kuma bukaci Majalisar tarayyar da ta gayyato Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da kungiyar ECOWAS da su shigo domin fara batun bai wa ’yan kabilar Ibon damar zabin kansu.

Ta kuma bukaci ’yan majalisar ataryyar da su dakatar da aikin yi wa tsarin mulkin 1999 kwaskwarima, wanda suka bayyana aikin da wanda ake yin sa a lokacin da bai dace ba lura da yadda ake tayar da jijiyar wuyan neman ballewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel