Kafofin yanar gizo na CNN, BBC da wasu manyan jaridun duniya sun daina aiki
1 - tsawon mintuna
Manyan gidajen yanar gizo na kafofin watsa labarai a duk duniya sun daina aiki a halin yanzu sakamakon wata matsala da suka samu.
Wasu daga cikin shafukan da aka gano a yanzu sun hada da: New York Times, CNN, Bloomberg, Guardian UK, BBC, Financial Times, Vanguard ta ruwaito.
Sai dai, wasu daga cikin rukunin yanar gizon duk da haka sun dawo aiki tare da wasu nau'ikan hidimar shafin ma'ajin su.
Dalilin daina aikin nasu a halin yanzu ba a san shi ba amma ana iya danganta shi da gaskiyar cewa kamfanin Amazon, AWS, da ke adana dunbum bayanan kafofin shi ke da matsala, in ji AlJazeera
Karin bayani nan kusa....
Asali: Legit.ng