Sojoji da ‘Yan Sanda sun hallaka wani Hatsabibin Sojan IPOB da ya addabi Kudancin Najeriya

Sojoji da ‘Yan Sanda sun hallaka wani Hatsabibin Sojan IPOB da ya addabi Kudancin Najeriya

- Jami’an tsaro sun kashe gungun ‘yan ta’addan IPOB/ESN a Jihar Imo

- Joseph Uka Nnachi da wasu yaransa hudu sun bukaci barzahu a jiya

- Wannan mutumi ya na cikin shugabannin sojojin ‘Yan ta’addan IPOB

Sojojin Najeriya da ke aiki a garin Owerri, jihar Imo, sun bankado wata ta’asa da ake neman ayi, inda ‘Yan IPOB suka shirya kai wa jami'an ‘yan sanda hari.

A wata sanarwa da mai magana da yawun bakin sojojin kasan Najeriya, Birgediya-Janar Mohamed Yarima, ya fitar jiya, ya ce an hallaka dakarun IPOB.

Jami’an tsaron sojoji da taimakon ‘yan sanda na kasa, sun hallaka wani babban sojan kungiyar IPOB, Joseph Uka Nnachi wanda aka fi sani da King of Dragons.

KU KARANTA: Gwamnatin Zulum ta rufe sansanin masu gudun hijira

Ana zargin cewa Joseph Uka Nnachi ne wanda ya rika tsara hare-haren da ake kai wa hukuma da jami’an tsaro a jihohin Kudu maso gabashin kasar nan.

Tun bayan mutuwar Ikonso a Afrilun 2021 a kauyen Awomama da ke garin Orlu a jihar Imo, Joseph Uka Nnachi ya ke jagorantar ta’adin kungiyar IPOB.

Bayan nasarar da jami’an tsaro suka samu wajen kashe wannan ja’iri da ake yi wa lakabi da King of Dragon, an hallaka wasu hudu daga cikin manyan yaransa.

Har ila yau, sanarwar ta ce an yi ram da wani daga cikin sojojinsa, wanda yanzu haka yana ba jami’an tsaro da muhimman bayanan da za su taimaka masu.

Sojoji da ‘Yan Sanda sun hallaka wani Hatsabibin Sojan IPOB da ya addabi Kudancin Najeriya
Sojojin kasan Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Amurka ta gurfanar da Onus a kotu, akwai yiwuwar ya shafe shekaru a kurkuku

Bayan haka, sojoji sun samu makamai da suka hada da bindigogin AK 47 hudu, da kuma mota kirar karamar bas ta Toyota Hiace, da ‘yan ta’addan suke hawa.

Sojojin kasan sun kuma samu alburushi da tarkacen kayan tsibbu a wajen ‘yan kungiyar ta IPOB.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng