Gwamna ya fatattaki mutum 1, 000 da ya ba mukami a ranar da ya cika shekara 6 a mulki

Gwamna ya fatattaki mutum 1, 000 da ya ba mukami a ranar da ya cika shekara 6 a mulki

- Gwamna David Umahi ya kori mutane 1, 000 da suke aiki da Gwamnatin Ebonyi

- Gwamnan Ebonyi ya bada wannan sanarwar a jawabin bikin cika shekara 6 a ofis

- Wasu daidakun hadimai da mukarraban gwamnatin jihar Ebonyi kadai suka sha

The Nation ta rahoto cewa gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori duka shugabannin da ke sa ido a kan hukumomi da ma’aikaitun gwamnati.

Mai girma gwamna David Umahi ya ce wannan mataki zai fara aiki ne ba tare da wata-wata ba.

Rahoton da muka samu ya bayyana mana gwamnan ya bada wannan sanarwa ne yayin da yake yi wa al’umma jawabin cika shekara shida a kan mulki.

KU KARANTA: Abin da ya hana Jiga-jigan PDP, ‘Yan Majalisa sauya-sheka a Ebonyi

Wadanda gwamnan ya sallama daga mukamansu, sun hada da ‘yan kwamitin da ke kula da ma’aikatu da ke aiki a duka kananan hukumomin jihar.

Wannan kora ya shafi jami’an gwamnati da masu bada shawara a mazabu 171 da ake da su a Ebonyi.

Har ila yau, matakin da Mista David Umahi ya dauka ya shafi daukacin manyan masu bada shawarwari wajen aiki a ofishin mai girma gwamna.

Jaridar nan ta Independent ta tabbatar da wannan rahoto dazu, ta ce adadin wadanda Dave Umahi ya kora daga gwamnatinsa sun zarce mutane 1, 000.

KU KARANTA: Ina tare da Buhari, duk da sabaninmu - Umahi

Gwamna ya fatattaki mutum 1, 000 da ya ba mukami a ranar da ya cika shekara 6 a mulki
Gov. Dave Umahi Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Korar ma’aikatan da gwamnatin Ebonyi ta yi, bai shafi wasu daga cikin hukumomin gwamnati ba.

Wadannda suka tsira daga korar sune ma’aikatan bangaren shari’a, da hukumar da ke kula da majalisa, hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin jiha.

Sauran ma’aikatan da suka sha suna aiki da hukumar EBSIEC mai alhakin gudanar da zabe. Gwamnan yace kore su ne saboda wasunsu na tare da PDP.

Sanarwar korar mukarraban ta zo kwana guda bayan gwamnan ya tsige mutum 73 da ke cikin majalisar zartarwa na jihar Ebonyi a ranar Alhamis da yamma.

Da wannan kora da gwamnan yake yi, ya na ganin ‘yan APC da suka rasa kujerun gwamnati za su samu damar yin rajista a matsayin ‘Ya ‘yan APC a mazabunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel