Da duminsa: Ayade da APC sun kwace sakateriyar PDP dake Cross River
- Gwamnan jihar Cross River da jam'iyyar APC sun kwace ofishin jam'iyyar PDP na jihar
- Kamar yadda aka gani da safiyar Asabar, jami'an tsaro sun mamaye ofishin inda ake ta fentin APC
- A cikin makon da ya gabata ne Ben Ayade ya koma APC daga jam'iyyar PDP, lamarin da bai yi wa PDP dadi ba
Da safiyar Asabar, ginin dake 142(a) kan babban titin Murtala Mohammed a garin Calabar wanda shine sakateriyar PDP na jihar Cross River, an yi masa fentin launin jam'iyyar APC.
Vanguard ta tattaro cewa ginin da aka san cewa sakateriyar PDP ne an ga jami'an tsaro sun mamaye shi kuma ana cigaba da fentin launin APC.
Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da gwamnan jihar, Farfesa Ben Ayde ya bar jam'iyyar PDP inda ya koma APC.
Daga nan kuwa bai sassauta ba sai ya koma ya mayar da ofishin jam'iyyar PDP zuwa na sabuwar jam'iyyarsa ta APC.
Karin bayani na nan zuwa...
KU KARANTA: Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga matukar damuwa a kan hatsarin jirgin sama da yayi ajalin shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji.
Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana alhinin da shugaban kasan ya shiga.
"A yayin addu'a ga Ubangiji da ya gafartawa rayukan masu kishin kasan, shugaban kasan yace wannan babban rashi ne yayin da dakarun sojin kasar nan suka zage wurin ganin karshen kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta," Shehu ya wallafa.
Asali: Legit.ng