2023: Kwankwaso ya gana da manyan PDP da Kwankwasiyya, daga dawowa daga Umrah
- Rabiu Musa Kwankwaso ya yi zama da Shugabannin PDP na jihar Kano
- Kusoshin Kwankwasiyya sun halarci wannan taro da aka gudanar a jiya
- An yi taron ne yayin da ake batun samun baraka a tafiyar Kwankwasiyya
A ranar Talatar nan ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi zama da shugabannin jam’iyyar PDP da manyan Kwankwasiyya.
Kamar yadda muka samu labari daga hadimin tsohon gwamnan, Hon. Saifullahi Hassan an yi wannan zama ne a ranar Talata, 18 ga watan Mayu, 2021.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zauna da jagororin jam’iyyar hamayyar da jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya, a lokacin da ake jita-jitar an samu sabani.
KU KARANTA: Jam’iyyar PDP za ta sasanta Sanata Kwankwaso da Tambuwal
Jaridar Daily Trust ta ce jagoran jam’iyyar adawar ya jagoranci wannan taro ne domin a dinke duk wasu baraka kafin a tunkari babban zabe mai zuwa na 2023.
Kafin yanzu akwai rade-radin da ke yawo cewa Dr. Yunusa Adamu Dangwani ya na kokarin jawo sabani a tafiyar Kwankwasiyya saboda ya yi takarar gwamna.
Tuni Dr. Yunusa Adamu Dangwani ya musanya cewa akwai kullaliya tsakaninsa da Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda ya rike wa jam’iyyar PDP tuta a zaben 2019.
Jiya Saifullahi Hasan a shafin Twitter ya rubuta: “Mai girma Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci taron shugabannin jam’iyyar PDP na jihar Kano.”
KU KARANTA: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal
Shugabannin PDP na Kwankwasiyya da ke fadin kananan hukumomi 44 na jihar sun halarci wannan taro a yau (18 ga watan Mayu) a titin Miller, garin Kano.
Shugaban PDP na jihar Kano, Shehu Sagagi, da ‘yan majalisarsa suna wajen wannan taron da aka yi.
Kwankwaso ya kira wannan taro ne kwana daya bayan dawowarsa daga kasar Saudi inda ya yi Umrah. Kafin nan ya ziyarci kabarin mahaifinsa, ya yi masa addu’a.
A kwanakin baya idan za ku tuna, an samu rashin jituwa tsakanin bangaren Sanata Kwankwaso da ‘yan bangaren Aminu Wali da ke tare da gwamna Aminu Tambuwal.
Kwankwaso ya zargi Tambuwal da katsalandan cikin harkokin jam’iyyar PDP a jihar Kano, ya ce gwamnan ya na goyon bayan wanda ya yi wa PDP zagon-kasa a 2019.
Asali: Legit.ng