IGP ya tura ‘Yan Sanda zuwa Kaduna a dalilin zanga-zangar da ‘Yan kwadago su ke yi

IGP ya tura ‘Yan Sanda zuwa Kaduna a dalilin zanga-zangar da ‘Yan kwadago su ke yi

- Shugaban ‘Yan Sanda na kasa ya tada Dakaru na musamman zuwa Kaduna

- IGP Usman Alkali Baba ya bada umarnin a tabbatar da zaman lafiya a jihar

- Hakan na zuwa ne bayan an soma yajin-aiki, ana ta zanga-zanga a Kaduna

Mukaddashin shugaban ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya umarci dakarunsa da cewa ka da su bari wani rikici ya barke a fadin jihar Kaduna.

A ranar Litinin, 17 ga watan Mayu, 2021, Usman Alkali Baba ya bada umarnin a kare rai da dukiyar mutane yayin da aka soma yajin-aiki a Kaduna.

IGP Usman Alkali Baba ya bada wannan umarni ne yayin da kungiyoyin kwadago suka soma yi wa gwamnatin Nasir El-Rufai zanga-zanga da yajin-aiki.

KU KARANTA: Yajin aikin NLC ya kankama a Kaduna, an rufe sakatariya

Umarnin da Usman Alkali Baba ya ba ‘yan sandan ya shiga hannun Daily Trust jim kadan bayan kungiyoyin kwadago sun dakatar da ayyuka a Kaduna.

Sufetan ‘yan sandan yake cewa ya zama dole a baza jami’an ‘yan sanda na musamman domin a karfafa tsaro a kan hanyar Kaduna zuwa birnin Abuja.

Babban jami’in da ke kula da yada labarai da hulda da jama’a na ‘yan sanda na kasa, Frank Mba, ya fitar da wannan jawabi, ya na sanar da AIGs da CPs.

Frank Mba ya sanar da manyan jami’an ‘yan sandan su tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.

IGP ya tura ‘Yan Sanda zuwa Kaduna a dalilin zanga-zangar da ‘Yan kwadago su ke yi
IGP da Shugaba Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: An yi ram da tsohon jami'in da yake horas da 'Yan IPOB

Ya ce:Bayan haka, IGP ya umarci AIG (mataimakan sufetocin ‘yan sanda) da kwamishinonin da ke jihohi da shiyyoyi da ke kula da hanyoyin Kaduna-Abuja da kewaye, su kare rai da dukiyoyin al’umma da ke karkashin duk yankunan da suke da iko."

Umarnin ya ba jami’an kar-ta-kwana umarni su shiga jihar Kaduna, da nufin tabbatar da tsaro.

“Haka zalika, mataimakin sufetan ‘yan sanda da ke kula da sashen samun bayanan sirri, ya bada umarni ayi maza a baza dakarun IRT da STS.” Inji Mba.

Za a yi hakan ne da nufin kwantar da duk wata tarzoma da ta za ta iya tashi a kan babban titin.

Dazu kun ji cewa kungiyar ASCAB ta goyi bayan yajin-aikin da aka shiryawa gwamnatin Nasir El-Rufai, ta yi kira ga Ma’aikatan Jihar Kaduna su yi bore.

Femi Falana ya na zargin Gwamnatin El-Rufai da jawo matsalar rashin tsaron da ake fama da shi. Falana yake cewa an kori mutane 60, 000 daga aiki a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel