Buhari: Manyan PDP sun gana da Janar Babangida, za ayi zama da Obasanjo, Jonathan

Buhari: Manyan PDP sun gana da Janar Babangida, za ayi zama da Obasanjo, Jonathan

- Shugabannin PDP sun ziyarci garin Minna, sun gana da Ibrahim Babangida

- A makon nan ne ake sa ran za a zauna da sauran tsofaffin shugabannin kasa

- Uche Secondus da mutanensa za su hadu da Bukola Saraki, da David Mark

‘Yan majalisar gudanarwa na jam’iyyar PDP, sun hadu da tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya.

Jaridar This Day ta rahoto cewa shugabannin jam’iyyar adawar za su yi wani zama da tsofaffin shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Har ila yau, ana sa ran ‘ya ‘yan majalisar NWC na jam’iyyar hamayyar za su tattauna da tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark.

KU KARANTA: Zargin cewa na nemi in daure El-Rufai, kanzon kuregensa ne - Jonathan

Hakan na zuwa ne bayan PDP ta bada sanarwar za ta zanta da masu ruwa da tsaki da ke duka bangarorin da ke kasar nan, domin ta ceto ‘Yan Najeriya.

Jam’iyyar ta na neman dabarar da za a bi, a kawo karshen matsalolin rashin tsaro na kashe-kashe da asarar dukiya da rayukan al’umma da ake yawan yi.

A karshen makon da ya wuce, Prince Uche Secondus, suka hadu da Ibrahim Badamasi Babangida, suka tattauna kan batun kasa a gidansa a Minna, Jihar Neja.

PDP ba ta fitar da wani jawabi a game da wannan zama da ta yi da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ba.

KU KARANTA: Matasan APC sun shirya addu'o'i a kan matsalar tsaro a Arewa

Buhari: Manyan PDP sun gana da Janar Babangida, za su yi zama da Obasanjo, Jonathan
Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewa Uche Secondus da ‘yan majalisarsa za su hadu da Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da David Mark a makon nan.

Shugabannin PDP sun kuma sa lokaci za su yi zama da Dr. Bukola Saraki da Anyim Pius Anyim. Dukkaninsu sun taba rike shugaban majalisar dattawa a baya.

Bayan duba yadda kasa ta ke ciki, ana tunanin Uche Secondus da sauran ‘Yan NWC suna wannan tattaunawa ne a kan abin da ya shafi sha’aninsu na cikin gida.

Kafin yanzu kun ji cewa majalisar PEAC mai bada shawara kan harkar tattalin arziki ta ba gwamnatin tarayya shawarwarin fita daga kangi a Najeriya.

PEAC ta sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa idan aka cigaba da biyan tallafin fetur, za a kai ga lokacin jihohi ba su da sisin kobo a lalitarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel