Babachir Lawal ya na marawa takarar Bola Tinubu baya a zaben 2023
Babban Jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya samu mubaya’a daga tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, game da zabe mai zuwa na 2023.
Babachir David Lawal a wata hira da ya yi ya bayyana cewa Bola Tinubu ne wanda ya fi dacewa ya karbi ragamar mulkin kasar nan bayan cikar wa’adin Muhammadu Buhari.
Ko da tsohon Jigon na gwamnatin Buhari bai nuna ya na goyon bayan mulki ya koma Kudancin Najeriya ba, amma ya jaddada cewa Tinubu ne wanda ya fi dacewa da rikon kasa.
Mista Babachir David Lawal ya bayyana wannan ne a hirar da ya yi da Jaridar Daily Sun, ya na cewa: “Ina rajin ganin wanda ya fi cancanta ya karbi mulki a hannun Buhari.”
“Kuma a yanzu, wanda ya fi dacewa da wannan shi ne Bola Ahmed Tinubu, wanda aka yi dace kuma ya fito daga Yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.” Inji David Lawal.
KU KARANTA: Ka da Buhari ya koma irin mulkin kama-karyan Hitler – Shehu Sani
Ya ce: “Na san shi sosai, kuma ba batun ya na Abokina ba. Abin da na sani game da shi, shi ne za ayi dace shugaban kasa idan ya hau mulki. Ya nuna cewa ya san shugabanci.”
“Ya rike Legas da kyau a lokacin da ya yi gwamna. Don haka ne duk Magadansa su ka bi tafarkinsa. Duk da an samu wasu ‘Yan ba-ni-na-iya, amma sun gane ya kafa tsari.”
“Mutane na iya zaginsa, amma shi ne ya kawo gwamnonin da ba a taba yin irinsu ba a tarihin Legas; Daga Tinubu, Fashola, Ambode zuwa Sanwo-Olu wanda ya fara mulki yanzu.”
“Wani abu da ‘Yan Najeriya za su duba shi ne akwai lokacin da a cikin majalisar FEC ta mutane 36, ya na da mutane hudu.” Sai dai Lawal bai iya kama sunan Ministocin nan ba.
Tsohon Sakataren gwamnatin ya tabo batun Gwamnoni da shirin Amotekun a hirar ta sa. Tun kafin hirar 2 ga Fubrairu, an saba jin Lawal ya na nuna goyon bayan Bola Tinubu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng