Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi da Kudinsu Yakai biliyan 80 a Cikin Watanni uku
- Hukumar NDLEA ta kama mutum 2000 cikin watanni uku, cewar Shugabanta Buba Marwa
- A cewarsa, an kama kwayoyi sama da kilo miliyan biyu cikin kankanin lokaci
- Hakan ya bayyana ne lokacin da Sifeton Yan Sanda ya kai masa ziyara
A kalla kilo miliyan biyu na miyagun kwayoyi, wanda kudin su ya kai Naira biliyan 80 hukumar NDLEA ta kama a cikin watanni uku.
Shugaban Hukumar, Burgediya Janaral Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin sufeto janar na mukaddashin 'yan sandan Nijeriya, Usman Baba Alkali a yayin ziyarar da ya kai hukumar ta NDLEA a ranar Laraba.
Marwa ya bayyanawa Alkali cewa hukumar ta samu nasarar kararraki sama da 300 a kotu, tare da nasarar kame masu laifi 2,000, a cikin kwanaki dari na shugabancin sa.
Wadannan nasarori a cewar Marwa, sun samu ne saboda karfin da hukumar ta bayar wajen kama masu safarar kwayoyi zuwa Nijeriya ko daga Nijeriya zuwa wata kasar.
Shugaban yace babu shakka idan aka samu hadin guiwa tsakanin NDLEA da hukumar 'yan sandan Nijeriya ta hanyar baiwa juna bayanan sirri, za'a samu karin adadin kame na miyagun kwayoyi da masu safarar su a Nijeriya.
"A yanzu sama da mutane miliyan 15 ne a Nijeriya suke ta'amuli da miyagun kwayoyi wanda a gaskiya adadin ya wuce kima, " Marwa yace.
KU DUBA: Matsalar tsaro: Lokacin tsige Buhari bai yi ba, Sanatan da yan bindiga suka addabi mazabarsa

Asali: UGC
KU KARANTA: Shahrarren Dan bindigan da ya tuba, Auwalu Daudawa, ya koma gidan jiya
A nasa bangaren, sufeta janar na 'yan sandan Nijeriya, Usman Baba Alkali yace akwai bukatar hadin kan aiki tsakanin hukumar 'yan sanda da NDLEA saboda a cewar sa, mafiya yawan masu aikata laifi a Nijeriya suna amfani ne da miyagun kwayoyi.
A saboda haka yace a shirye suke don bada cikakken hadin kai ga hukumar fada da miyagun kwayoyi a yayin gudanar da ayyukan ta don tabbatar da tsaro da kawar da miyagun kwayoyi a cikin al'umma.
A bangare guda, Hukumar tsaron farin kaya DSS ta ce yan kungiyar IPOB da hukumar tsaron da suka kafa ESN sun sayi bama-bamai da suke niyyar tayar da tarzoma da su a jihar Imo.
Hukumar ta ce ta samu labarin leken asiri cewa yanzu haka ana tafiyar da bama-baman dake jihar Legas zuwa karamar hukumar Orlu, a jihar Imo, The Punch ta ruwaito.
DSS ta bayyana hakan ne a wasikar da ta aikewa Kwamandan Artillery Brigade, Obinze, Owerri, Imo.
Asali: Legit.ng