Matsalar tsaro da Rashin hanyoyi masu kyau: Ahmed Musa ba zai buga wasannin 'Away' ba, Kano Pillars
-Ahmad Musa ya ba zaiyi musharaka a wasannin da za'a buga a wajen Kano ba
-Shugaban kungiyar Kano pillars, Surajo Yahaya ne ya tabbatar da haka
-Yahaya ya bayyana cewa Ahmed zai buga dukkan wasannin gida amma ba zai halarci yawancin wasannin waje ba
Kyaftin na Super Eagles kuma sabon dan wasan kungiyar Kano Pillars, ba zai buga yawancin wasannin waje ba a sashe na biyu na kakar NPFL da za'a fara ranar 28 ga Afrilu.
Punch ta ruwaito cewa Ahmed Musa ya bayyanawa shugabannin Kano Pillars cewa ba zai samu daman musharaka a wasannin da za'a buga ba a jihar Kano ba.
Shugaban kungiyar, Surajo Yahaya ya tabbatar da cewa sabon dan wasan zai iya buga dukkan wasannin gida, amma ba zai halarci yawancin wasannin waje ba.
"Ahmed Musa babban dan wasa ne kuma dubi ga yadda halin tattalin arzikin kasar nan da hanyoyi marasa kyau. Zai buga dukkan wasannin gida kuma idan akwai jirgi a jihar, zai halarci wasannan waje," Yahaya yace.
KU KARANTA: An rusa majalisar dokoki, an rufe iyakoki, an saka dokar ta baci a Chadi
KU KARANTA: 'Yan bindigan da suka sace daliban Kaduna suna bukatar N500m
A bangare guda, Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyarsa ta wasanni ta miliyoyin naira a Kaduna inda ake sa ran matasa za su samu horo kuma za su iya baje kolin baiwarsu ma.
Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Leceister City yana daya daga cikin attajiran yan wasan Najeriya idan aka yi la’akari da kadarorin sa tun lokacin da ya fara wasan kwallon kafa daga titin garin Jos.
Ahmed Musa ya fara wasan kwallon kafa a garin Jos kafin ya koma kungiyar JUTH FC daga inda tsohon zakaran gasar kwallon kafa ta Kano Pillars ya sanya masa hannu.
Asali: Legit.ng