Gyadar doguwa: Ubangiji ne ya yi ba zan mutu a sanadiyyar hadarin jirgi ba inji Gwamna Ganduje

Gyadar doguwa: Ubangiji ne ya yi ba zan mutu a sanadiyyar hadarin jirgi ba inji Gwamna Ganduje

- Dr. Abdullahi Ganduje ya tuno hadarin jirgin da ya kashe Abdullahi Wase a 1996

- A wancan lokacin Gwamnan ya na Kwamishina, an shirya za ayi tafiya da shi

- Wani uzuri ya taso, a dalilin haka Gwamna Ganduje bai bi tawagar gwamnan ba

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada labarin yadda hadarin jirgin sama ya yi sanadiyyar mutuwar tsohon gwamna Kanal Abdullahi Wase.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce Allah ne ya yi ba da shi za a mutu a hadarin jirgin da ya kashe tsohon gwamnan Soja, Abdullahi Wase da mukarrabansa ba.

Jaridar Daily Trust ta ce Abdullahi Umar Ganduje ya bada wannan labari ne a lokacin da ya karbi bakuncin jakadiyar Najeriya a Romaniya, Barista Safiya Nuhu.

KU KARANTA: An kaddamar da littafin tarihin Aisha Buhari, shugaban kasa ba ya Najeriya

Safiya Nuhu wanda mutumiyar jihar Kano ce, ta na cikin wadanda wannan hadarin jirgin sama ya shafa, domin shi ne ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinta.

Ya ce: “An shirya cewa ni kai na, a lokacin ina kwamishinan ayyuka, sufuri da gidaje, zan ziyarci masallacin Juma’a na Wase wanda aka gina a lokacin.”

“Ni ne ke nemo gudumuwar gina masallacin. Aka tsara cewa gwamna zai yi tafiya ya kaddamar da ginin, sannan ya yi ta’aziyyar rasuwa da aka yi.” Inji Ganduje.

“Ni na shirya yadda za a yi tafiyar. Na nemo jirgin saman da za a hau, jirgin na Alhaji Aminu Dantata ne. Na rubuta sunayen wadanda za su tafi tare da gwamna.”

Gyadar doguwa: Ubangiji ne ya yi ba zan mutu a sanadiyyar hadarin jirgi ba inji Gwamna Ganduje
Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Ganduje
Asali: UGC

KU KARANTA: Ozekhome ya ce Gwamnatin Buhari ba ta yi da kowa sai ‘Yan Arewa kurum

Ganduje ya ce: “A da mahaifinki ba ya ciki, a lokacin da zan bar gidan gwamnati, sai ya zo ya ce mani meyasa ba a sa sunansa a cikin wadanda za su yi tafiyar ba?”

Kamar yadda Ganduje ya bayyana, a haka aka sa sunan mahaifin Jakadiyar Najeriyar cikin wadanda za su yi wannan tafiya da sai dai aka dawo da gawarsu.

Dr. Ganduje ya ce an shirya za ayi tafiyar kenan sai wata matsala ta bijiro, a dalilin haka, bai samu bin tawagar gwamna Wase ba, sai kwatsam ya ji sun yi hadari a Jos.

Kwanakin baya idan za ku tuna, Abdullahi Ganduje, ya je ya yi ta'aziyya a gidan marigayi Makaman Karaye, mahaifin tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso.

Alhaji Musa Sale Kwankwaso ya rasu ne a Disamban 2020 ya na da shekara 93. Gwamna Ganduje ya jajantawa iyalan mamacin a gidansu dake garin Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel