Badakala da almundahana: ICPC ta sanar da neman tsohon hadimin Buhari 'ruwa a jallo'

Badakala da almundahana: ICPC ta sanar da neman tsohon hadimin Buhari 'ruwa a jallo'

Hukumar yaki da cin hanci da rasha wa a tsakanin jami'ai da ma'aikatan gwamnati (ICPC) ta bayyana neman Mista Okoi Obono-Obla, tsohon hadimin shugaba Buhari, ruwa a jallo bisa zarginsa da aikata zamba da cin hanci.

Shugaba Buhari ne ya nada Obon-Obla a matsayin shugaban kwamitin kwato kadarorin gwamnatin tarayya (SPIP)

A cikin jawabin da ta fitar ranar Talata, kakakin hukumar ICPC, Rasheedat Okoduwa, ta ce jama'a sun shigar da jerin korafe-korafe a kan rawar da Obono-Obla ya taka yayin da yake jagorantar kwamitin SPIP.

Hukumar ICPC ta ce ta yanke shawarar bayyana neman Obono-Obla ruwa a jallo ne saboda ya ki amsa gayyatar da ta yi masa domin bayar da bayani a kan zarge-zargen da ake yi masa.

ICPC ta kara da cewa ta samu korafe-korafe masu yawa a kan yadda Obono-Obla ya ci amanar da aka damka masa, fantama wa da dukiya fiye da abinda yake samu da kuma karbar nagoro daga hannun mutanen da kwamitinsa yake zargi da laifi tare da kuma gudanar da bincike a kansu.

Okoduwa ta bayyana cewa ICPC ta gudanar da bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa Obono-Obla, inda ta gano cewa tabbas ya saba wa wasu tanade-tanaden hukumar wanda aka kirkira a shekarar 2000.

"Mun gayyace shi don ya bayyana a gabanmu domin bayar da bayanai a kan zargin da ake yi masa, amma ya yi burus tare da share gayyatar ba tare da kuma ya bayar da wani uzuri ba," a cewar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel