Da duminsa: APC ta samu karuwa, dan majalisar wakilai ya sauya sheka
Wani dan majalisar wakilan tarayya, Hon Jimoh Yusuf, a ranar Laraba ya sauya sheka jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).
Hon Jimoh Yusuf na wakiltan mazabar Egbado North/Imeko Afon na jihar Ogun.
A wasikar da Kakakin majalisa ya karanta a zauren majalisar, dan majalisar ya ce ya fita daga ADC ne sakamakon rikice-rikicen dake faruwa a jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.
Dan majalisan ya jinjinawa gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, saboda shi ya gamsar da shi ya koma APC.
Amma mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar, Toby Okechukwu, yace sauya shekarsa ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce wasikar da dan majalisar ya aike akwai tafka da warwara saboda a bangare guda ya ce rikicin jam'iyyar ADC ta tilasta masa fita, sannan kuma yace gwamnan jiharsa ya gamsar da shi.
Asali: Legit.ng