Matata Chioma ta kamu da coronavirus - Shahararren mawaki, Davido

Matata Chioma ta kamu da coronavirus - Shahararren mawaki, Davido

Chioma, masoyiyar shaharraren mawakin Najeriya Davido ta kamu da kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da coronavirus kamar yadda mawakin ya bayyana a shafinsa ta dandalin sada zumunta na Instagram.

A cewar mawakin wanda a baya-bayan nan ya dawo daga kasar Amurka, ya tafi ya yi gwajin kwayar cutar ta Covid-19 tare da matarsa da wasu hadimansa da suka dawo tare domin su tabbatar ba su dauke da kwayar cutar tun da suka dawo a ranar 25 ga watan Maris.

A cikin 'yan kwanakin nan ne Chioma ta dawo daga birnin Landon kuma sakamakon gwajin ya nuna ta harbu da kwayar cutar amma mawakin da dansu ba su kamu ba.

Shahararren mawakin ya rubuta cewa matarsa tana dauke da kwayar cutar duk da cewa a halin yanzu ba ta fara nuna wasu alamu ba amma dai an killace ta.

Matata Chioma ta kamu da coronavirus - Shahararren mawaki, Davido
Matata Chioma ta kamu da coronavirus - Shahararren mawaki, Davido
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Ba abinda ya shafi jama'a bane - FG ta yi martani a kan lafiyar Abba Kyari

"Ni ma zan kebe kai na na tsawon kwanaki 14," kamar yadda ya rubuta inda kuma ya yi wa masoyansa godiya bisa addu'o'i da fatan alheri da suke masa.

A baya dai Davido ya soke wasar da zai yi a yankin Amurka ta Yamma da aka shirya yi a watan Maris da Afrilun saboda bullar annobar ta coronavirus.

Soyayyar shi da Chioma ya fito fili na a bara yayin da ya fara saka ta cikin bidiyon wakokinsa. Daya daga cikin wakokinsa da suka yi suna sosai kuma ya fito da ita shine waka mai taken 'Assurance'

A makon da ya gabata, mawakin ya fitar da bidiyon wakarsa mai taken '1milli' inda aka hasko masoyan yayin daurin aure na gargajiya.

Sun haifi dan su na farko ne a watan Oktoban shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164