Yayin kokarin cetosu an raunata wasu dalibai, har yanzu ana neman 30: Gwamnatin jihar Kaduna

Yayin kokarin cetosu an raunata wasu dalibai, har yanzu ana neman 30: Gwamnatin jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce har yanzu bata san inda dalibai 30 na kwalejin zamanantar da gandujin daji dake Afaka, karamar hukumar Igabi na jihar Kaduna suke ba.

Mun bayyana muku yadda Sojoji suka ceto dalibai 180.

A jawabin da kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce ma'aikatarsa ta samu labari kuma ta ankarar da Sojoji.

"Sojojin sun samu nasarar ceto mutum 180; 42 dalibai mata, ma'aikata takwas da kuma dalibai maza 130. Har yanzu akwai dalibai maza da mata 30 da bamu san inda suke ba," yace.

Ya ce wasu daga cikin daliban da aka ceto sun jigata kuma suna jinya a asibitin Sojoji.

Ya kara da cewa gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar ya mika godiyarsa ga jami'an.

Yayin kokarin cetosu an raunata wasu dalibai, har yanzu ana neman 30: Gwamnatin jihar Kaduna
Yayin kokarin cetosu an raunata wasu dalibai, har yanzu ana neman 30: Gwamnatin jihar Kaduna Credit: @MobilePunch
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng