Kungiyar Dattawan Arewa ta yi wa Gwamnonin da su ke rigima da juna a fili fada

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi wa Gwamnonin da su ke rigima da juna a fili fada

- Kungiyar dattawan Arewa ta ja-kunnen Gwamnonin da su ke rikici a fili

- NEF ta ba Gwamnonin shawara su dinke barakar dake tsakaninsu a daki

- Ana samun sabani tsakanin Gwamna Samuel Ortom da Bala Mohammed

Kungiyar dattawan Arewa watau NEF, ta bada shawara ga gwamnonin jihohin yankin da su guji fito wa su na maida wa junansu kalamai a idanun kowa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto kungiyar NEF ta na cewa fadan da wasu gwamnonin su ke yi a fili zai bar mummunan tarihi ga mutanen Arewacin Najeriya.

Darektan hulda da jama’a da wayar da kan mutane na NEF, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana haka yayin jawabi a gaban manyan Arewa a taron Kaduna.

A ranar Alhamis ne gwamnoni da sarukunan Arewa su ka yi zama da wakilan gwamnatin tarayya a garin Kaduna, inda aka tattuna a kan sha’anin rashin tsaro.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace 'Yan makaranta kusan 300 a Zamfara

“Gwamnoni shugabanni ne, duk lokacin da su ka yi sabani a fili a kan yadda za a tunkari matsalar tsaro ko yakar ‘yan bindiga, zai jawo mutane su kara shiga dar-dar.”

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce: “Mu na rokon shugabanninmu, dole a samu yadda za a shawo kan sabanin da ya ke tsakanin gwamnoni ba tare da an fito fili ba.”

Baba-Ahmed ya yi kira ga gwamnonin Arewa su hada kai da takwarorinsu na bangaren Kudu domin a kare dukkan mutanen Arewa da ke zaune a can yankin.

Tsohon sakataren na din-din-din ya ce kungiyar NEF za ta roki Ubangiji ya ba gwamnonin sa’a.

KU KARANTA: Akeredolu zai yi kokarin maida Gwamnan Edo jam’iyyar APC

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi wa Gwamnonin da su ke rigima da juna a fili fada
Hakeem Baba Ahmed Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce shawara su ke ba shugabanni ba adawa ba; “NEF ba za ta gaza sukar shugabannin mu ba, muddin ta ga cewa abubuwa ba su tafiya yadda su ka kamata.”

A jiyan kun ji cewa Malam Nasir El-Rufai ya fadi abin da ya hada Gwamnonin Bauchi da na Benuwai fada a fili, ya ce sabanin fahimta ne ya shiga tsakaninsu.

A taron na jiya, El-Rufai ya tsoma bakinsa kan cacar bakin da ake yi tsakanin gwamna Bala Mohammed na Bauchi, da kuma gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.

Gwamnan ya ce kawunan duka abokan aikinsa ya hadu a kan haramta gantali da dabbobi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng