Sheik Gumi: ya kamata a tuhume shi saboda ya zama malamin ƴan garkuwa da mutane
-Da alama yawan shiga tsakani da Gumi ke yi ya fara ƙoƙarin sanya shi cikin wani hali.
-A a baya dai an samu wani rahoto na furucinsa kan matsayin masu garguwa da mutane kan cewa ba fa ƴan ta'adda ba ne.
-Wata ƙila wannan ne dalilin da ya sa aka fara sauya tunani kan malamin, inda Ƙungiyar Arewa (Norther Group) ta buƙaci da ai bincike a kansa.
Legit.ng ta rawaito cewa Asheik Gumi dai ya samu yabo daga wasu ƴan Najeriya kan namijin ƙoƙari da yake yi wajen tattaunawa da ƴan ta-da-zaune-tsaye.
KARANTA WANNAN: Ba zan taba baiwa masu kiran Fulani da 'yan ta'adda hakuri ba, Gwamnan Bauchi
Ga abin da Binniyat ya ce,
"Ya gaya musu cewa sojojin da ke kashe su ba Musulmai ba ne. Ya kuma gaya musu cewa a duk sa'ilin da za su kai hari na ramako, to su riƙa tantancewa da kyau. Ya nuna rashin jin daɗinsa game da yadda wasu ƙungiya ƴan ta-da-zaune suka yi garkuwa da wata mata mai sanye da hijabi da ɗanta."
Sannan ya ƙara da cewa, "ka ga ni, malamin na ƙoƙarin yin abu kamar mai ba su fatawa. Kuma in har akwai buƙatar tattaunawar to ya kamata ta zama saboda samar da adalci ne."
KARANTA WANNAN: Su Burutai su gode wa Allah ba lokacin da muke majalisa ba ne jI shehu sani
Yana cike da mamakin yadda Gumi ya kasance marar sha'awar adalci da bin kadi na waɗanda aka zalinta, amma ya fi damuwa da walwala da samar da ƴanci masu aikata ɓarna.
Kaka kuma ya roƙi gwamnatin tarayya da ta ba da kariya ga Fulani masu garkuwa da mutane da ma sauran masu ɗauke da bindugu a Kudancin ƙasar.
Gumi ya ba da wannan shawara ne a ranar Lahadi 21 ga watan Fabarairu. Malamin dai dake zaune a Kaduna ya nuna cewa su fa ƴan ta-da-zaune-tsayen nan ƴan Najeriya ne, ba baƙin haure ba ne.
A bangare guda, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce ba zai taba bada hakuri ba a kan tsokacin da yayi a makon da ya gabata ga wadanda ke kwatanta 'yan kabilar Fulani da makasa ko masu garkuwa da mutane.
Idan za a tuna, gwamnan ya fuskanci manyan kalubale tare da caccaka bayan da yace makiyaya na da damar yawo da bindiga kirar AK-47 domin baiwa kansu kariya.
Mohammed wanda yayi jawabi a ranar Laraba yayin kaddamar da kamfen din yi wa dabbobi riga-kafi na 2020/2021 wanda aka yi a Galambi da ke jihar Bauchi.
Asali: Legit.ng