Sabon jami'i mai tsaron shugaban ƙasa (ADC) ya kama aikinsa a yau a Abuja

Sabon jami'i mai tsaron shugaban ƙasa (ADC) ya kama aikinsa a yau a Abuja

- Shugaba Buhari ya yi sabon dogari yayinda tsohon ke neman karin girma a gidan soja

- Kanal Abubakar ne ADC mafi dadewa tare da wani shugaban kasa a tarihin Najeriya

- Buhari ya yi bankwana da Abubakar yayin da sabon dogarin, Dodo, ya kama aiki

A ranar Litinin ne dai sabon Jami'in Tsaron Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, laftanar Kanar Yusuf Dodo ya kama aikinsa a fadar shugaban ƙasa.

Sabon Jami'an dai ya maye gurbin kanar Mohammed Lawal Abubakar wanda ke tsaron lafiyar shugaban tun farkon wa'adinsa na mulki a shekarar 2015.

Sabon jami'i mai tsaron shugaban ƙasa (ADC) ya kama aikinsa a yau a Abuja
Sabon jami'i mai tsaron shugaban ƙasa (ADC) ya kama aikinsa a yau a Abuja
Source: Twitter

KARANTA WANNAN: 'Yar Atiku Abubakar ta sabunta rajistarta na jam'iyyar APC

Abubakar ya bar aikin ne dai a yau saboda tafiya ƙasar Santiago a Chile domin yin kwas na wata biyar a kan Tsare-tsare na Harkokin Tsaro daga ranar 8 ga watan Maris.

Wasu kafofi sun sanar da wani gidan talabijin cewa kwas ɗin na da alaƙa ne da tabbatar da samun ƙarin girmansa zuwa matsayin burgediya Janar.

Kafin dai tabbatar da shi a sabon matsayin nasa, Laftanar kanar Dodo yana riƙe ne da babban muƙami a makarantar horon sojoji da ke Kaduna (Nigerian Defence Academy).

KARANTA WANNAN: Minista ta dakatar da Sarki saboda ‘hada kai da masu garkuwa da mutane’ a Abuja

A ƙarshe dai tsohon jami'in tsaron tare da matarsa da ƴarsa sun miƙa wannan nauyi ga sabon jami'in a wani ƙaramin shagali na taya murna da aka shirya masa.

A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce Najeriya ce ta fi kowacce kasa talauci a duniya, Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya yi wannan bayanin ne a lokacin da aka kaddamar da Hukumar Kula da Kare Lafiyar Jama’a a jihar ranar Talata.

Ya ce gwamnatinsa ta kafa hukumar ne don tabbatar da cewa duk shirye-shiryen kare zamantakewa an isar da su cikin hadaka, mai kunshe da ci gaba.

Source: Legit.ng

Online view pixel