Gumi: Masu garkuwa da mutane ba ƴan ta’adda ba ne kuma Izuwa yanzu mutane ƙalilan suka kashe

Gumi: Masu garkuwa da mutane ba ƴan ta’adda ba ne kuma Izuwa yanzu mutane ƙalilan suka kashe

-Sanan nan malamin adinin Musulunci Sheik Gumi ya yi magana a kan masu garkuwa da mutane tare da yin wasu kalamai masu ɗaure kai.

-Sanin kowa ne cewa garkuwa da ɗalibai ya zama ruwan dare, inda suke tambayar kuɗin fansa mai yawan gaske.

-Saidai wannan malami ya bayyana cewa suna irin abun nan ne mai kama da ramuwar gayya wanda bai ga laifin hakan kai tsaye ba idan a kai duba da ra'ayinsa.

Babban shehin malamin nan Ahmad Gumi ya bayyana cewa ƴan bindiga ba ƴan ta’adda ba ne domin faɗansu; “faɗan cikin gida”.

Ya dai yi wannan lafazi ne a wata hira da yayi da gidan wani talabijin a ranar Litinin inda ya tabbatar da cewa ƴan bindigar ba sa sha’awar kisan mutane, kuma ko da ƴan kaɗan ɗin da suka kashe, sun yi ne ba a bisa son ransu ba.

A wasu jihohi dai na Arewa maso yamma da kuma Arewa maso tsakiyar ƙasar nan, ana ta fama da cigaba da samun hare-hare na ƴan bindiga waɗanda ke zagayawa ƙauyuka suna kai farmaki a yayin da ba sa kan hanyoyi kamar yadda suka saba domin sace matafiya.

Gumi dai ya nuna cewa su ƴan bindigar sun fi sha’awar karɓar kuɗaɗen fansa, sannan sukan saurari mutane idan ana so a gana da su.

KU KARANTA: cbn da wasu za su habaka tsarin gudanar da kasuwar bitcoin

“Suna dai yin gargukuwa ne domin su sami kuɗi. Dubi yadda suka saki mutane maƙare a motar bas bayan sun buƙaci kuɗin fansa na naira miliyan 500, amma bayan tattaunawa da su, sai suka sake su ba tare da an biya ko sisi ba.”

Gumi kenan a wani hoto tare da masu garkuwa da mutane
@thecable.ng
Gumi kenan a wani hoto tare da masu garkuwa da mutane @thecable.ng
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa, “sannan ana kiran su da Fulani masu kashe mutane, amma mutum nawa suka kashe?” Sannan, “idan sun yi kisan ma, to ba a bisa son ransu ba ne, wataƙila wanda ya mutum ma marar lafiya ne. Amma ku gaya min mutum nawa suka kashe? Ƴan kaɗan ne fa.”

Da aka yi masa tambaya a kan ƙauyuka da suke ƙonewa, sai ya nuna cewa ai suna yi ne domin ramuwa.

KA KARANTA: yar atiku abubakar ta ta sabunta registarta na jamiyyar apc

“Wannan ba wai don ta’addanci ba suke yi ba, suna yi ne don ramuwa irin na ƙabilanci. Sannan ba sa taɓa kai hari wani ƙauye idan ba a taɓa musu wani nasu ba.”

Sannan shehin malamin ya yi wa mutane gargaɗin cewa, idan fa matsin da ake wa ƴan bindigar ya yi yawa, to fa Boko Haram na iya yin nasarar jawo su cikin su.

“Ina cike da fargabar Boko Haram na iya jan ra’ayinsu, domin mun ga yadda suke ta ƙoƙarin shiga cikinsu. Amma izuwa yanzu su ɗin ba ƴan Boko Haram ba ne.”

A bangare guda, Manoma a jihar Filato sun caccaki gwamnan jihar Simon Lalong kan zargin da yake musu na mallakar bindigogi kirar AK-47 kamar yadda Fulani makiyaya suke, jaridar Punch ta tattaro.

Lalong ya bayyana haka ne lokacin da yake magana a shirin gidan talabijin na Channels TV, Sunrise Daily a ranar Talata, ya ce ba daidai bane a tasa Fulani makiyaya a gaba kadai ba da zargin mallakar bindigogin AK-47 kasancewar manoma ma suna dashi.

Haka nan, Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Filato (AFAN), John Wuyep, ya bayyana kalaman a matsayin zunzurutun karya.

Sauke sabuwar manhajarmu a wayarka: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafinkanmu na sada zumunta:

Fesbuk (Facebook): https://facebook.com/legitnghausa

Tuwita (Twitter): https://twitter.com/legitnghausa

Za ku iya ba mu sahihin labarinku ta hanyar turowa ta: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel