Sanata Stella Oduah ta ci zaben Sanatar Anambra ta Arewa da kuri'u 113,989

Sanata Stella Oduah ta ci zaben Sanatar Anambra ta Arewa da kuri'u 113,989

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana tsohuwar ministar harkokin zirga zirga Sanata Stella Oduah a matsayin wacce ta lashe zaben mazabar sanatar Anambra ta Arewa. Ta samu kuri'u 113,989, inda ta yiwa Allah godiya akan sake zabarta a karo na biyu.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben a ranar Litinin a Onitsha, jami'in tattara sakamakon zaben mazabar, Farfesa Hugh Maduka, ya ce Oduah ta jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 113,989, wanda ya ba ta damar lallasa sauran 'yan takara 20.

Ya ce Mr Emmanuel Chinedu na jam'iyyar APGA ya zo na biyu da kuri'u 59,937 yayin da Mr Nelson Onubogu na jam'iyyar APC ya zo na ukku da kuri'u 11,995.

Jami'in hukumar INEC, ya ce Mr Chinedu Ekwealor na jam'iyyar YPP ya zo na hudu da kuri'u 1,024.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Orji Uzor Kalu ya lashe zaben sanatan Abia ta Arewa

Sanata Stella Oduah ta ci zaben Sanatar Anambra ta Arewa da kuri'u 113,989
Sanata Stella Oduah ta ci zaben Sanatar Anambra ta Arewa da kuri'u 113,989
Asali: Facebook

Ya yi nuni da cewa an gudanar da zaben cikin luma a mafi yawan kananan hukumomin mazabar, sai dai akwai wasu yankuna da aka samu matsalar satar akwati da kuma kona akwatinan da wasu 'yan ta'adda suka yi.

Da ya ke tsokaci kan wannan nasara da ta samu, Odua ta ce samun nasarar tazarce a karo na biyu ya nuna irin kaunar da Allah ke yi mata da kuma al'ummar mazabar

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel